Arsenal ta amince za ta dauki dan wasan Chelsea, Kai Havertz kan fam miliyan 65.
Ana cewar bayan da kungiyoyin suka cimma yarjejeniya, kenan abin da ya rage shine amincewar dan wasan daga nan a gwada lafiyarsa.
Wata kila kudin sayen dan kwallon tawagar Jamus zai karu har da na tsarabe-tsarabe, wanda ya ci wa Chelsea kwallo tara a karawa 47 a kakar da ta wuce.
Havertz, mai shekara 24, ya koma Chelsea daga Bayer Leverkusen a 2020 kan fam miliyan 71.
Shine ya ci kwallon da Chelsea ta lashe Champions League a 2021, bayan doke Manchester City.
Mikel Arteta na kokarin kara karfin 'yan wasan Arsenal, bayan da kungiyar za ta buga Champions League a kaka mai zuwa.
Haka kuma Arsenal ta taya dan wasan West Ham, Declan Rice karo biyu, bayan da Gunners ta yi tayi na biyu fam miliyan 90 ranar Talata.
Chelsea na kokarin rage yawan 'yan wasan da take da su, wadda ta amince Mateo Kovacic ya koma Manchester City kan fam miliyan 30.
Haka kuma dan wasan tawagar Faransa, N'Golo Kante, mai shekara 32 ya amince zai koma Al-Ittihad ta Saudi Arabia idan kwantiraginsa ya kare a karshen watan Yuni.