BBC Hausa of Thursday, 22 June 2023

Source: BBC

Arsenal ta taya Jurrien Timber na Ajax kan fam miliyan 30

Arsenal ta taya dan kwallon Ajax, Jurrien Timber kan fam miliyan 30. Arsenal ta taya dan kwallon Ajax, Jurrien Timber kan fam miliyan 30.

Arsenal ta taya dan kwallon Ajax, Jurrien Timber kan fam miliyan 30.

Ana alakanta dan wasan da kungiyoyin Premier League da yawa ciki har da Manchester United.

Timber mai shekara 22 dan kwallon tawagar Netherlands yana da saura yarjejeniyar kaka biyu a Ajax.

Ajax na bukatar kudin dan wasan fiye da tayin da Arsenal ta yi, amma ana cewar ba za a samu matsalar amincewa daga dan wasan ba idan har Ajax ta amince.

Arsenal wadda ta kare a mataki na biyu a teburin Premier League a kakar da aka kammala na sa ran kammala cinikin dan kwallon.

Wasu kungiyoyin da suka hada da Bayern Munich tana daga cikin mai son sayen dan wasan kan fara kakar bana.

Timber ya buga wa wasa 47 a dukkan karawa a kakar da ta wuce a Ajax, har da wasa shida da ya yi a Champions League.

Ya bayar da gudunmuwar da Ajax ta lashe babban kofin tamaula na Netherlands a 2021 da kuma a 2022.

Dan kwallon ya buga wa tawagar Netherlands karawa 15 har da wasa hudu a gasar cin kofin duniya a Qatar da kasar ta kai quarter finals a 2022.

Kociyan Arsenal, Mikel Arteta na son kara karfin gurbin masu tsare bayan Gunners, domin kaka mai zuwa da akwai kalubale da yawa.

Ba a da tabbas kan makomar Thomas Partey da Granit Xhaka, bayan da Gunners ta taya dan kwallon West Ham, Declan Rice.