BBC Hausa of Tuesday, 8 November 2022

Source: BBC

Arsenal za ta yi cefane, za a sa Liverpool kasuwa, dan Kamaru  ya ki Man Utd, Chelsea ta samu dama

Yan wasan Arsenal Yan wasan Arsenal

Masu Liverpool, Fenway Sports Group za su sayi  matashin dan wasan tsakiya dan Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, daga  Borussia Dortmund a kan fan miliyan 87 kafin su sayar da kungiyar. (Marca, via FourFourTwo)

Manchester United da Chelsea na daga cikin kungiyoyin da ke son Bellingham, amma shi kuwa ba ya son zuwa Stanford Bridge. (TeamTalk)

Hamshakin attajirin Birtaniya Sir Jim Ratcliffe na daga cikin wadanda ake sa ran za su sayi kungiyar ta Anfield. (Liverpool Echo)

Sama da rabin kungiyoyin Premier sun tura wakilansu kallon wasan Ajax da PSV Eindhoven ranar Lahadi, inda dan wasan gaba na gefe na PSV Cody Gakpo, ya kasance daya daga cikin wadanda suka taka leda. (90min)

Damar Chelsea ta daukar dan wasan gaba na AC Milan Rafael Leao, ta karu saboda takaddamar da ke tattare da maganar tsawaita kwantiragin dan kwallon na Portugal. (Sky Italy, via Mirror)

Arsenal da Tottenham na duba yuwuwar sayen matashin dan wasa mai kai hari na Lille, Jonathan David mai shekara 22, dan kasar Kanada. (GiveMeSport, via TeamTalk)

Jagorar gasar Premier, Arsenal ta shirya kashe kudi a watan Janairu domin yin cefane mai kyau saboda ta ci gaba da rike wuta a kadamin da take kai na neman cin kofin gasar a yanzu. (90min)

Manchester United na son sayen dan wasan gaba na Bayern Munich kuma dan Kamaru Eric Maxim Choupo-Moting a watan Janairu, amma kuma dan wasan mai shekara 33 ya fi son zama a kungiyarsa ta Jamus. (Florian Plettenberg)

Kwararren mai bayar da shawara na Brentford Jack Wilson zai bar kungiyar domin ya koma wurin zakarun Premier Manchester City. (Athletic) 

Kociyan kungiyar Luton Town Nathan Jones na shirin zama sabon mai horad da ‘yan wasan Southampton bayan da kungiyar ta Premier ta kori Ralph Hasenhuttl ranar Litinin. (Mail)

To amma Southampton na sha’awar kociyan Brentford Thomas Frank sannan kuma kungiyar ta tattauna da kociyan River Plate Marcelo Gallardo. (Guardian)