Aston Villa ta amince ta ɗauki ɗan ƙwallon Leicester, mai taka leda daga tsakiya Youri Tielemans.
Dan wasan tawagar Belgium, mai shekara 26, zai koma Villa Park ranar 1 ga watan Yuli, lokacin da yarjejeniyarsa za ta ƙare a Leicester City.
Bayan da Leicester City ta fadi daga Premier League zuwa buga Championship a baɗi, an yi ta alakanta Tielemans da ƙungiyoyin Arsenal da Manchester United da kuma Roma.
Tielemans - wanda shi ne na farko da Villa ta fara ɗauka kawo yanzu don shirin tunkarar kakar wasa mai zuwa - ya koma Leicester a 2019, inda ya taimaka wa ƙungiyar ta ɗauki FA Cup a 2021.
Tielemans ya fara buga wasannin aro a Leicester daga Monaco a Janairun 2019, daga baya ƙungiyar ta saye shi a matakin mafi tsada kan fam miliyan 40 a shekarar a cikin watan Yuli.
Ya buga wa Belgium gasar cin kofin duniya a 2018 da 2023 da kuma Euro 2020.
Tielemans ya koma Villa wadda ta yi ta bakwai a teburin Premier League da aka ƙarƙare, inda za ta buga gasar zakarun Turai ta Europa Conference League.