Masana harkokin siyasa a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu kan kalaman ɗan takarar shugaban ƙasar ƙasar a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, na buƙatar haɗin kan sauran jam'iyyun hamayya domin kawar da APC mai mulki.
Masana irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge suna da ra'ayin samun haɗakar jam'iyyu masu ƙarfi ka ya zama wani tagomashi ga siyasar Najeriya.
A baya a cewar Farfesan sai da jam'iyyar da Atiku ke takara a cikinta ta PDP ta shafe shekara 16 tana mulki a ƙasar, amma ƙawancen da aka samu mai ƙarfi ya haifar da jam'iyyar APC da ta ƙalubalance ta kuma har ya zuwa yanzu ita take mulki.
To amma game da kiran da Atiku ya yi, Farfesa Fagge ya ce, "ya so ya ɗan makara saboda tuntuni kiran da ake sha'awa a ga 'yan siyasar sun fito sun yi a karan kansu amma a lokacin da aka so hakan ba ta samu ba.
"Son zuciya da buƙata irin ta raɗin kansu ta hana manyan 'yan siyasa da jam'iyyun adawa su zo su haɗa kansu waje ɗaya su yi hakan".
A fahimtar Farfesan wasu jam'iyyun ba za su amsa wannan kira na Atiku ba, ganin cewa jam'iyyun ba su suka nemi haka ba a buƙatar kansu.
Na biyu kuma ya ce zaɓe ya yi nisa yanzu, akwai kimanin shekara uku zuwa uku da rabi ta ta yi saura, don haka haƙurin dunkulewa wuri guda ka iya zama da kamar wuya a wurin jam'iyyun.
A tsarin siyasa irin ta Najeriya "akan ji ɗuriyar jam'iyyun siyasa ne kawai a lokutan zaɓe, amma bayan zaɓe ba a wani damu da tasirunsu ba.
"Kiran da ya yi wasu ba za su yarda ba, saboda a siyasar Najeriya ko wanne ɗan takara ya fi so ya yi mulki ba ya taimaka waninsa ya yi ba".
Farfesa ya ce wani abu da zai ƙara sa firgici a sauran jam'iyyun da aka nemi haɗin kansu shi ne, "yadda Atiku yake tsalle daga wannan jam'iyya zuwa waccen, sannan wadda duk yake ciki shi ke fitowa a matsayin ɗan takara" wannan zai sake haifar da rashin aminci tsakaninsu.
Idan an yi maja wane ne zai janye wa wani takara?
Wannan na ɗaya daga cikin tambayoyin da ke waɗari a zukatan 'yan Najeriya.Kuma amsar wannan tambaya ita ake gani za ta iya tabbatar da haɗakar za ta yi wu ko kuma akasin haka.
Fafesa Kamilu Sani Fagge ya ce "anan ne gizo ke saƙar, tunda ba a gina siyasar Najeriya ba a kan wata aƙida ko manufa ba, illa kawai a haɗu ne domin a kama mulki".
Mutane da yawa sun so Atiku da wasu su janye su barwa wani, ganin cewa jam'iyyarsu ta PDP ita ta fara gabatar da batun karɓa-karɓa a ƙasar, in ji Farfesa Fagge.
Babu shakka haɗakar za ta iya zama barazana ga jam'iyyar APC mai mulki a ƙasar, idan an samu jam'iyyu masu karfi.
Ya ƙara da cewa amma matuƙar ba a samu wannan haɗin kai mai ƙarfi ba, "APC za ta iya sama da shekarun da PDP ta yi tana mulki a baya".
Har yanzu ba a makara ba - Martanin Atiku
Atiku Abubakar ya ce babu wata makara da aka yi game da neman wannan haɗin kai da jam'iyyun siyasa.Ta bakin mai taimakawa tsohon shugaban Najeriyan na musamman Abdurrashin Uba, Atiku ya ce akan yi kura-kurai kuma a zo a gyara su a cikin tafiya, to abin da ya faru kenan a zaɓen da ya gabata.
A cewar Abdurrashid Uba "zaɓukan da aka yi a jihohin Bayelsa da Imo da ke cike da kura-kurai, sun sake bayyana buƙatar da ake da ita ta haɗin kan jam'iyyu wajen kawar da APC."
Ya ce tsarin da APC ta ke neman ɗauka shi ne na mayar da Najeriya mai jam'iyya guda, wanda kuma ba za su amince da hakan ba.
Atiku ya ce daga yanzu ƙofarsa abuɗe take domin haɗa hannu da duk jam'iyyar da take son haɗa gwiwar da shi.