Atletico Madrid ta sake daukar dan kwallon tawagar Faransa, Antoine Griezmann daga Barcelona kan kwantiragin da zai kare a 2026. Griezmann ya zama na shida mafi tsada a tarihi a duniya a lokacin da Barcelona ta dauke shi kan £108m a 2019 daga Atletico. Ya kuma ci kwallo 35 a wasa 102 da ya yi wa Barcelona, wadda ta bayar da shi aro ga Atletico kan yarjejeniyar kaka biyu. Mai shekara 31 ya ci kwallo uku ya kuma bayar da biyu aka zura a raga a bana, wasa uku daga ciki aka fara tamaula da shi, sauran daga baya ake saka shi. Wani rahoto daga mai fashin bakin tamaula dan Sifaniya, Guillem Balague ya ce a lokacin da Grizmann ya koma aro an shimfida ka'idar cewar Atletico za biya fam miliyan 40 idan har ya buga wasa minti 45 a sama da kaso 50 cikin 100 na fafatawar kungiyar. Hakan ne ya sa kociyan Atletico Madrid, Diego Simeone baya fara wasa da Griezmann sai dai ya yi canji, bayan minti 60 da fara tamaula sau 11 a bana. Simeone ya yi hakan ne don kada su sayi dan kwallon kan yadda aka gindaya ka'ida tun farko, har yarjejeniyarsa ya kare a kungiyar Camp Nou. Griezmann zai fara wasa na farko a matakin dan kwallon Atletico a karawar Champions League da za ta yi da Club Brugge ranar Laraba. Dan wasan da ya lashe kofin duniya da Faransa a 2018 a Rasha, shi ne na hudu a kan gaba a cin kwallaye a tarihin kungiyar. Ya ci kwallo 144 a wasa 304 a karo biyu da yake taka leda a Atletico Madrid tun bayan da ya koma kungiyar daga Real Sociedad a 2014. Zaman da ya yi a Atletico ya lashe Europa League da Spanish Super Cup da kuma Uefa Super Cup.