Wani bincike da BBC ta kwashe tsawon shekara ɗaya tana gudanarwa ya bankaɗo asirin wata ƙungiya mai azabtar da birrai a duniya wadda ke harkoki a tsakanin Indonesia zuwa Amurka.
BBC ta samu ɗaruruwan kwastomomi a Amurka da Birtaniya da sauran wurare da ke biyan 'yan ƙasar Indonesiya don azabtarwa da kashe jariran birrai jinsin macaques masu doguwar jela ana ɗauka a bidiyo.
Kungiyar azabtarwar ta fara gudana ne a YouTube, kafin ta koma wasu zauruka na musamman a dandalin Telegram.
Yanzu haka dai ‘yan sanda na bin wadanda ke da hannu cikin lamarin kuma tuni aka kama wasu da dama.
Gargadi: Wannan labarin ya kunshi wasu bayanen da za su iya tayar da hankali
'Yan jaridar BBC sun boye a cikin daya daga cikin manyan kungiyoyin azabtarwan na Telegram, inda daruruwan azzalumai suka taru don fito da munanan hanyoyin azabtarwa tare da ba da izini ga mutane a Indonesia da sauran kasashen Asiya don aiwatar da su.
Burin azzaluman shi ne su hada fina-finan na musamman, inda ake cin zarafin jariran birai masu dogayen wutsiya, ana azabtar da su, wasu lokutan kuma a kashe su yayin da ake dauka a bidiyo.
BBC ta bi diddigin duka wadanda ake azabtarwan a Indonesia, da masu rarrabawa da masu saye a Amurka, kuma ta samu damar yin amfani da hukumomin tabbatar da doka na kasa da kasa don tabbatar da sun fuskanci fushin hukuma.
Akalla mutane 20 ne ake gudanar da bincike a kan su yanzu a duniya, ciki har da mata uku da ke zaune a Birtaniya da ‘yan sanda suka kama a bara aka kuma sake su yayin da ake cigaba da gudanar da bincike, sai kuma wani mutum daya a jihar Oregon ta Amurka da aka gurfanar da shi a makon jiya.
Mike McCartney, babban mai rarraba bidiyo a Amurka wanda aka fi sani da sunanan, 'The Torture King', ya amince ya yi magana da BBC, kuma ya bayyana lokacin da ya shiga kungiyar azabtar da birai ta Telegram.
McCartney ya ce: "Sun yi shirin kada kuri'a." "Ka na son ka yi amfani da guduma? ko kana son ka saka filaya? Kuna son sukundireba?" Bidiyon da ya fito shi ne "abu mafi tayar da hankali da na taba gani," in ji shi.
McCartney, tsohon memban gungun 'yan babur wanda ya kwashe lokaci a gidan yari kafin ya shiga duniyar azabtar da birai, ya kare yana gudanar da kungiyoyin Telegram da yawa inda masu sha'awar azabtarwa suka rarraba bidiyo.
"Ba shi da bambanci da kudin miyagun kwayoyi," in ji shi. "Kudin miyagun kwayoyi na fitowa daga hannye masu kazanta, wannan kudin yana fitowa ne daga hannayan da ke lullube da jini."
Har ila yau, BBC ta gano wasu manyan mutane biyu da ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka (DHS) ke binciken su - Stacey Storey, wata kaka mai shekaru 47 daga Alabama wacce aka fi sani da 'Sadistic' a cikin al'umma, da kuma wani jagora wanda aka fi sani da 'Mr Ape' - wanda ba za mu iya bayyana ainihin sunansa ba saboda dalilai na tsaro.
A wata hira da BBC 'Mr Ape' ya bayyana cewa ya kashe akalla birai hudu tare da azabtar da wasu da dama. Ya ba da umarnin wallafa bidiyo masu dauke da "mummunan zalunci", in ji shi.
Jami’an ma’aikatar tsaron cikin gida sun kwace wayar Storey, inda suka zakulo kusan bidiyon azabtarwa guda 100, da kuma shaidun da ke nuna cewa ta biya kudin kirkirar wasu bidiyo mafi muni da aka taba wallafawa.
A cewar majiyoyin 'yan sanda, Storey ta kasance a cikin kungiyar azabtarwan cikin kwanan nan kamar farkon wannan watan. Da BBC ta tuntube ta a Alabama a watan Janairu, Storey ta yi ikirarin cewa an yi mata kutse, kuma ta ki yin cikakken bayani kan zargin.
'Mr Ape', da Stacey Storey da Mike McCartney su ne uku daga cikin muhimman mutanen da ake hari a cikin binciken da hukumar tsaron cikin gida ke gudanarwa.
Har yanzu ba a tuhume su ba, amma za su iya fuskantar daurin shekaru bakwai a gidan yari idan aka gurfanar da su bisa ga shaidar da hukumar ta DHS ta tattara.
Jami'i na musamman Paul Wolpert, wanda ke jagorantar binciken hukumar DHS, ya ce duk wanda ya dubi lamarin daga bangaren jami’an tsaro ya yi matukar kaduwa da irin laifukan da ake zargin.
"Ban sani ba ko akwai wanda zai iya shirya tunkarar irin wannan laifin ba," in ji shi. "Haka kuma da lauyoyi da alkalai, da kuma duk wanda ya karanta cewa hakan na faruwa, ina tunanin dole sai ya firgita."
Duk wanda ke da hannu wajen siya ko rarraba bidiyon azabtar da biri ya kamata "ya yi tsammanin za a kwankwasa masa kofa wani lokaci", in ji Wolpert. "Ba zai tsira ba."
'Yan sanda a Indonesia sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da azabtarwa.
An tuhumi Asep Yadi Nurul Hikmah da laifin azabtar da dabbobi da kuma sayar da nau'in dabbobi masu kariya, an yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.
An yanke wa M Ajis Rasjana hukuncin watanni takwas - mafi nauyin hukuncin da za a iya yankewa mai laifin azabtar da dabba.
Har yanzu ana iya samun bidiyoyin azabtar da birai a Telegram da kuma Facebook, inda a baya-bayan nan BBC ta samu kungiyoyi da dama suna musayar abubuwan da suka wuce gona da iri, wasu na da mambobi sama da 1,000.
Sarah Kite, wacce ta kafa wata kungiyar agaji na kula da dabbobi mai suna 'Action for Primates' ta ce " Yawan wadannan munanan bidiyon sun karu, wadanda a baya a boye suke amma yanzu suna yawo a fili a kan dandali daban daban kamar Facebook."
Kamfanin Facebook ya shaida wa BBC cewa an cire kungiyoyin da muka jawo hankalin kamfanin garesu.
"Ba mu yarda da habaka cin zarafin dabbobi a kan dandalinmu ba kuma muna cire wannan abun a duk lokacin da muka gano shi, kamar yadda muka yi a wannan yanayin," in ji mai magana da yawun kamfanin.
Ms Kite ta kuma yi kira da a sabunta dokokin Burtaniya domin a samu saukin gurfanar da mutanen da suka biya kudin wallafa bidiyon azabtarwa.
"Idan wani yana da hannu dumu-dumu wajen haifar da wannan illar ta hanyar biyan kudi da kuma samar da jerin abubuwan da suke so a yi wa dabba, ya kamata a samar da dokoki masu karfi da za su dauki mataki a kan su," in ji ta.
Kamfanin YouTube ya shaida wa BBC a cikin wata sanarwa cewa cin zarafin dabbobi ba shi da "wuri" a dandalin kuma kamfanin "yana aiki tukuru don kawar da abubuwan da ba su da kyau a cikin gaggawa".
Sanarwar ta ce "A wannan shekarar kadai, mun cire dubban daruruwan bidiyoyi tare da dakatar da dubban tashoshi saboda karya manufofin mu na abubuwa masu tayarda hankali."
Kamfanin Telegram ya ce "ya himmatu wajen kare sirrin mai amfani da dandalin da kuma kare hakkokin bil'adama kamar 'yancin fadin albarkacin baki", ya kara da cewa ma’aikatansu "ba za su iya yin sintiri a kungiyoyi masu zaman kansu ba’’