BBC Hausa of Thursday, 7 December 2023

Source: BBC

Ba mu da rabuwar kai a United - Ten Hag

Kocin Manchester United Ten Hag tare da yan kwallon sa Kocin Manchester United Ten Hag tare da yan kwallon sa

Kocin Mnchester United Erik ten Hag ya yi watsi da raɗe-raɗin cewa an samu rabuwar kai a Old Trafford, yana mai jaddada cea ƙungiyar na tafiya kan turbar da ta dace.

Da ƙwallo biyun da Scott McTominay ya zira a ragar Chelsea a wasan da suka tashi 2-1 ranar Talata, shi ne karon farko da ƙungiyar ta Ten Hag ta ci wata ƙungiya da ke cikin goman farko a Premier da ake yi yanzu.

Kocin ya ce da Manchester sun yi amfani da damar da suka samu a wasan da bai wahalar da su ba kamar yadda suka fuskanta – yayin da shi kuma kocin Chelsea Mauricio Pochettino ya ce United ta cancanci samun nasara a wasan.

Ten Hag ya yi farin ciki da sakamakon wasan bayan wuyar da ya sa a hannun Newcastle da ta janyo magoya bayan United suka yi ta surutai marasa dadi.

“Saɓani? a’a ba dai a wajenmu ba,” in ji Ten Hag. “ A nutse muke. Kuma ƙungiyar na tafiya kan tafarkin da ya dace.

“Ba wai ɓacin rai ba ne, amma da munci ƙwallo da dama da wasan ya mana sauki. Muna sauyawa sosai, muna iya kare kanmu, muna muna da hazaƙa muna farin ciki da yanayin da muke ciki.”

Wannan ce nasara ta shida da United ta samu a cikin wasa takwas da ta yi a Premier, duk da cewa ɗan wasan da ya ci kwallon McTominay ya maimaita gyaran da tsohon ɗan wasan ƙungiyar mai sharhi Patrice Evra ya yi – wanda ya ce “ka da wani abu ya ɗauki hankalinmu”.

Wannan ne karo na biyu da McTominay ya ci ƙwallo biyu a Old Traffod. Da wannan ya zama wanda ya fi kowa cin ƙwallo a United inda ya ci kwallo biyar a wannan kakar.