BBC Hausa of Monday, 8 May 2023

Source: BBC

'Ba mu da tabbacin abin da zai faru da mu idan muka isa Port Sudan'

Tun farkon rikicin gwamnatin Najeriya ta shirya kwashe mutanenta zuwa Masar Tun farkon rikicin gwamnatin Najeriya ta shirya kwashe mutanenta zuwa Masar

Ɗalibai ƴan Najeriya sama da 1500 ne ke kan hanyar zuwa birnin Port Sudan, a yunƙurin gwamnatin kasar na ɗebe jama'arta da yaƙin Sudan ya ritsa da su.

Tun farkon rikicin ne gwamnatin Najeriya ta tsara kwashe jama'arta zuwa Masar daga nan kuma a ɗebo su zuwa gida.

Sai dai matsaloli da dama da suka baibaye aikin musamman rashin samun izinin shigar da su Masar ya sa hukumomin Najeriyar sauya shawarar kai su iyakokin Habasha da Port Sudan.

Shugaban Ƙungiyar ɗaliban Najeriyar da ke karatu a Sudan, Abubakar Babangida ya shaida wa BBC cewar kimanin motoci 27 ne suka ɗebe ɗaliban jami’ar Razi da ta Afrikiya a Sudan, a daren Lahadi, don kai su Jedda, zuwa Najeriya.

Ya ce "kowace bas tana ɗauke da mutum 50 zuwa 55".

A cewarsa, aikin kwashe mutanen bai shafi ɗalibai kaɗai ba har ma da ƴan Najeriyar da ke zaune a Sudan.

Abubakar Babangida ya ƙara da cewa kawo yanzu suna ƙauyen Adbara da ke da nisan kilomita 7 da Port Sudan, sai dai ya ce suna cikin fargaba saboda rashin jami’an gwamnati ko ɗaya da ke jagorantar motocin nasu, ga kuma ƙarancin kuɗin abinci da wasu ke fama da shi.

Shugaban ɗaliban ya kuma yi ƙarin bayani game da hatsarin da aka samu na wata gobara da ta tashi a ɗaya daga cikin bas-bas ɗin da aka kwashi mutane.

"Babu asarar rayuka kuma babu rauni ko ɗaya, sojoji ne suka taimaka musu suka kashe wutar, su 30 da wani abu ne a cikin motar, sai aka riƙa ɗaukar su cikin bas bas har aka kwashe su gaba ɗaya.

Mece ce makomar ɗaliban da suka isa Port Sudan?

"Daman tsare-tsaren da ake yi.... su waɗanda suka bi ta Egypt suna can ta Egypt ɗin ba mu san tsarin ba, daga nan jirgi ne za a ɗauka, jirgin ruwa ne za a shiga zuwa Jeddah, ƙila sai mun ƙarasa sai su hukumomi su faɗa mana abin da za mu yi." in ji Shugaban ɗaliban.

Game da abinci da samun kulawa kuma, shugaban ɗaliban ya ce iya ruwa fidda kai saboda kowa da kuɗinsa yake saya, "idan baka da kuɗi, wani ɗan uwanka ya taimaka maka ko abokinka ko wani wanda ya sanka."

"Mu kaɗai muke tafiya babu wani jami'in tsaro ko ɗaya da yake tare da mu." in ji shi.

Babu jami'an gwamnati tare da mu...

Shugaban ɗaliban ya bayyana cewa a tsawon tafiyar da suke yi, babu wani jami'in dioflomasiyya da yake tare da su.

"Jiya da muka bar Khartoum ƙarfe 12 na dare, babu wani jami'in diflomasiyya da muke tare da shi, amma yau sun ce za su taso da asuba, ba mu sani ba idan suka zo za su tsaya wajenmu ne ko a a'." kamar yadda ya faɗa.

Masar ta sa sharuɗan shigar da ɗaliban Najeriya ƙasarta

A cewar Jakadan Najeriya a Masar, Ambasada Nura Abba Rimi ya shaida wa BBC cewa Masar ta gindaya wasu sharuɗa da ta ce sai an cika su kafin ta bai wa ƴan Najeriyar da aka kwaso daga Sudan izinin shiga ƙasarta.

Ya ce ƙa'idojin su ne:

1 a. Cikakken bayani kan ranakun da jiragen da za su kwashi ɗaliban za su shiga ƙasar.

b. Adadin mutanen da jiragemn za su iya ɗauka.

c. Alƙawarin cewa da zarar yan Najeriya sun bar iyakar ƙasar, za a kai su ne tashar jirgin da za a kwashe su.

2. Jerin sunayen mutanen da aka kwashe da lambobinsu na Paspo.

3. Sahihan takardun paspo.

4. Kasancewar jami'an gwamnatin Najeriya a wuraren kwashe su zuwa jiragen da alka tanada.

5. Motocin bas bas da aka tanada da za su kwashe ƴan Najeriyar zuwa filin jirgin sama.