Mikel Arteta ya ce ba wasan da zai fuskanci Manchester City ne zai fayyace ko Arsenal za ta lashe Premier League na bana ba.
Arsenal tana matakin farko a kan teburi da tazarar maki biyar tsakaninta da kungiyar Pep Guradiola da za su kece raini ranar Laraba a Etihad.
Sai dai City tana da kwantan wasa biyu, bayan da Gunners ta yi canjaras uku a jere a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Arsenal ta tashi 2-2 a gidan Liverpool da wanda ta yi 2-2 da West Ham da kuma 3-3 da ta kara da Southampton duk a Premier League.
''Mun san za mu ziyarci Etihad ranar Laraba, wasa ne mai sarkakiya, amma ko shine zai fayyace makomarmu a Premier League? A'a.'' in ji Arteta
''Muna da kwarin gwiwa, na kuma kalli yanayin 'yan wasanmu bayan kammala fuskantar Southampton, muna bukatar kofin nan, za mu nuna hakan ranar Laraba.''
''Amma dole sai mu saka kwazo, saboda abin da ake bukata kenan a kakar nan ta bana.''
Rabon da Arsenal ta dauki kofin Premier League tun kakar 2004 karkashin Arsene Wenger.
''Idan mun ci wasa ranar Laraba ba wai mun dauki kofin bane, domin zai rage saura wasa biyar, karawa biyar komai zai iya faruwa a tamaula.'' in ji Arteta.
''Mun kwan da sanin cewar a kakar nan City da Liverpool sun kankane Premier League, domin rawar da suka taka shekara shida da ta wuce - shi ya sa muke kokarin yin kafada da kafada da su.''
Arteta ya sanar cewar Granit Xhaka, wanda bai buga karawa da Southampton ba, saboda rashin lafiya, da kyar idan zai yi wasan na Etihad.
Har yanzu William Saliba bai murmure ba a raunin da ya ji a Europa League a karawa da Sporting Lisbon tun cikin watan Maris.