Babban jami'in Manchester United, Richard Arnold zai sauka daga muƙaminsa kamar yadda BBC ta fahimta.
Mai shekara 52 ya maye gurbin Ed Woodward a matsayin mai babban muƙamin mahukuntan ƙungiyar a watan Fabrairun 2022.
Ba a sanar da tabbacin barin ƙungiyar ba, a lokacin da Sir Jim Ratcliffe mai rukunin kamfanin Ineos da ke daf da sayen kaso 25 cikin dari na hannun jarin United.
Ana sa ran za a kammala cinikin a cikin watan nan na Nuwamba, lokacin da ake buga wasa na kasa da kasa.
Ana cewa Ineos Group na shirin biyan kusan fam biliyan 1.25 kudin hannun jarin marasa rinjaye, wanda ake fatan kammala komawa a makon nan.
Arnold ya karɓi aikin babban jami'in United a Agustan 2007, wanda ya yi aiki a matakin darakta daga 2013 har zuwa lokacin da ya maye gurbin Woodward.
Shi ne ya kula da ɗaukar Erik ten Hag a 2022, kociyan da ya ci wa United Carabao Cup, kofin farko da ta lashe bayan shekara shida a kakarsa ta farko.
To sai dai United United na fuskantar ƙalubale a kakar 2023/24, wadda aka doke wasa tara daga 18 da ta buga a dukkan fafatawa.