BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Barca na son Ndidi, Arsenal na tattaunawa da Watkins ana shirin saye Man United

Wilfred Ndidi Wilfred Ndidi

Barcelona na tunanin zawarcin dan wasan tsakiya na Najeriya Wilfred Ndidi, mai shekara 26, lokacin da kwantaraginsa na Leicester City zai kare a karshen kakar wasa ta bana. (Sport Spanish)

Daraktan wasanni na Arsenal Edu ya tattauna da wakilin dan wasan Aston Villa Ollie Watkins game da daukar dan wasan na Ingila mai shekaru 27, yayin da Chelsea ma ke zawarcinsa. (Football Transfers)

Aston Villa na ci gaba da tattaunawa kan tsawaita kwantiragin Watkins kuma tana son a kammala sabuwar yarjejeniyar a watan Janairu. (90 Min)

Arsenal da Chelsea na son bayar da ‘yan wasa da kudi a yunkurinsu na sayen dan wasan gaban Ingila mai shekara 27 Ivan Toney daga Brentford, wanda ake ganin za su iya saya fan miliyan 75 jimlatan. (90 Min)

Newcastle United na shirin bude tattaunawa da dan wasan tsakiya na Brazil Joelinton, mai shekara 27, da dan wasan tsakiyar Ingila Sean Longstaff, mai shekara 25, kan tsawaita kwantiraginsu, da zai kare a watan Yunin 2025. (Insider Football).

Barcelona na tunanin zawarcin dan wasan tsakiya na Najeriya Wilfred Ndidi, mai shekara 26, lokacin da kwantaraginsa na Leicester City zai kare a karshen kakar wasa ta bana. (Sport Spanish)

Napoli na zawarcin tsohon kocin Paris St-Germain Christophe Galtier sakamakon rashin fara kakar wasa ta bana a karkashin Rudi Garcia da kafar dama. Ita ma Marseille na zawarcin kociyan mai shekaru 57, bayan ya yi murabus daga Marcelino a wani al’amari da y aba da mamaki. (90 Min)

Attajirin nan dan kasar Birtaniya Sir Jim Ratcliffe, ya ce a shirye yake ya sake fasalin tayin sa na siyan Manchester United domin cimma yarjejeniya da mamallakinta na yanzu Glazers. (Mirror)

Barcelona da Manchester City sun amince da wata yarjejeniya da ba a kai ga rubutawa ba, domin canja kwantiragin dan was an baya na Portugal mai shekaru 29 Joao Cancelo ya zaman a din-din-din. (El Chiringuito TV)

Dan wasan Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 20, ya ce ya yi magana da Manchester United a lokacin bazara kafin ya bar Red Bull Salzburg, amma yana jin komawa RB Leipzig ne ya fi dacewa don ci gabansa. (Transfermarkt)