Shugabanin majalisun jihohi 36 na Najeriya sun bayyana kalaman da mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar sanata Ovie Omo Agege, ya yi a kan cewa sune ke hana ruwa gudu a kokarin da ake na yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, da cewa yunkuri ne na bata musu suna. Senata Agege, a yayin wani taron manema labarai a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ya ce, har yanzu akwai majalisun jihohi 25 a kasar da ba su bayyana matsayarsu a kan kudirin doka 44 da aka aika musu wadanda ake son sauyawa a wajen gyaran kundin tsarin mulkin ba. Sannan kuma sun kawo wasu kudurori hudu da suka ce sai an saka su a cikin gyaran kafin su amince da wadancan 44. Wannan kalamai ne ya sa shugaban kungiyar shugabannin majalisun jihohin jihar, RT Hon. Abubakar Sulaiman ya mayar da martani a kai. Cikin wata hira da ya yi da BBC, RT Hon. Abubakar Sulaiman, ya ce kokarin bata mana sunan da muka fahimci sanata Ovie Omo Agege ke son yi, ya sa dole muka fitar da sanarwa don kare kanmu. Ya ce,” Ko shakka babu batun da ya ce mun rubuta takarda, kwarai mun rubuta, kuma tun lokacin da aka fara kokarin gyaran kundin tsarin mulkin muke son ganin an shigar da abubuwan da suka dace wa jihohi, saboda mu ne muka san damuwar da ke jihohin.” ‘’ Idan har da gaske gyaran ake son yi ai ya kamata a ce an saka abubuwan da za su kare mutuncin jihohi da kuma al’umarmu.” Shugaban kungiyar shugabannin majalisun jihohin, ya ce akwai abubuwan da suka tura kama abin da ya shafi batun samar da ‘yan sandan jihohi da abubuwa da dama har ma da batun neman kare kujerar kakakin majalisa daga tsigewar da ake yi musu a lokaci guda. Wadan nan su ne abubuan da muka tura muka ce muna so a sanya su a cikin gyaran kundin tsarin mulkin, to amma tun daga turo mana da amsar cewa za a yi wani abu akai, har yanzu shiru. Mu babban abin da ya bata mana rai shi ne da ya fito ya na cewa mun hana ruwa gudu, in ji shi. Ya ce, ‘’ Mu ana mu bangaren bai san kokarin da muke na ganin mun yi nazari a kan kudurin doka 44 da ake son sauyawa a wajen gyaran kundin tsarin mulkin ba, so muke mu duba sannan mu aika da amincewarmu, to amma kwatsam don a bata mana suna sai muka ji an ce wai mu ne ke hana ruwa gudu.” RT Hon. Abubakar Sulaiman, ya ce menene laifunsu, a ciki, su ba su ce ba za su aika da amincewarsu ba, suna duba wa ne. Ya ce,” Dama ko da muka rubuta na mu abubuwan da muke son a sanya a wajen gyaran kundin tsarin mulkin, mun ce sai mun ji daga garesu kafin mu duba na su, kuma koda aka aiko mana cewa an gani kuma za a duba, shi ke nan sai muka ci gaba da nazari a kan kudurin doka 44.