Aston Villa ta doke Brentford 4-0 a wasan mako na 13 a gasar Premier League da suka kara a Villa a Park ranar Lahadi. Villa ta buga wasan na babbar gasar tamaula ta Ingila a karon farko a bana tare da kociyan rikon kwarya, Aaron Danks. Villa ta sallami Gerrard ranar Alhamis 20 ga watan Oktoba, bayan da Fulham ta ci 3-0 a wasan Premier League karawar mako na 12. Wannan shi ne karon farko da aka ci kwallaye uku cikin sauri karkashin sabon koci kuma a ranar farko da ya ja ragamar kungiya. Cikin minti 14 da fara wasa Villa ta zura kwallo uku a ragar Brentford, inda minti biyu da take leda Leaon Bailey ya fara cin kwallo. Danny Ings ne ya kara na biyu a minti bakwai, sannan ya ci na uku na biyu a wasan a bugun fenariti a minti na 14. Bayan da aka koma zagaye na biyu ne Ollie Watkins ya ci Brentford kwallo na hudu. Villa ta kori Gerrard, wanda ta dauka aiki ranar 11 ga watan Nuwambar 2021, bayan jan ragamar wasa 40 da cin karawa 13 da canjaras takawas aka doke shi fafatawa 19. Wasa biyu kacal tsohon dan wasan Liverpool ya yi nasara a bana, shi ne wanda ya doke Everton da Southampton da canjaras uku.