BBC Hausa of Friday, 14 July 2023

Source: BBC

Biliyoyin kuɗin da aka amince wa ƴan majalisar Najeriya na tayar da ƙura

Majalisar dokokin Najeriya a Abuja Majalisar dokokin Najeriya a Abuja

Amincewar da zaurukan majalisar dokokin tarayya biyu suka yi da kuɗi naira biliyan 70 don tallafa wa kansu na tayar da ƙura a Najeriya.

Wasu ƴan Najeriya a shafin Tuwita sun tuhumi lokacin da aka amince da kuɗin, musamman ganin lamarin ya zo ne sama da wata ɗaya bayan gwamnatin ƙasar ta cire tallafin man fetur.

Cire tallafin man fetur ya haifar da tsadar sufuri da tashin farashin kayan abinci.


"Akwai wakilci na jam'iyya bakwai a Majalisar Dokokin Tarayya, ciki har da LP da PDP da kuma NNPP. Duk da haka babu ɗaya daga cikin ƴan majalisar da ya ƙi amincewa da batun naira biliyan 70 a wannan lokaci na tsanani. Za ku iya ganin cewa ƴan siyasar Najeriya ba sa faɗa idan aka zo batun kuɗi."

Wasu sun koka a kan cewa kuɗaɗen har sun zarce naira biliyan 19 da aka ware don tallafa wa manoman da ambaliyar ruwa ta tagayyara a damunar da ta wuce.

Ambaliyar ta yi sanadin mutuwar mutum 600 da raba sama da miliyan ɗaya da gidajensu.

Kuɗaɗen da majalisar ta amince wa kanta na cikin ƙaramin kasafin kuɗin da majalisar ta yi wa garambawul, wanda kuma ya ƙunshi naira biliyan 500 da za a ware domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Serap ta yi barazanar kai ƙara gaban kotu matuƙar ba a janye kuɗin da ƴan majalisar suka amince wa kansu ba.


"LABARI DA ƊUMI-ƊUMI: Cire Tallafi: Dole ne gwamnatin Tinubu ta janye kuɗi naira miliyan 70 na 'inganta aikin' sabbin ƴan Majalisar Dokokin Tarayya, da aka ware ba bisa ƙa'ida ba. Za mu haɗu a kotu idan ba a janye su ba."

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ambato ƴan majalisar na kare batun amincewa da kuɗin, inda suka ce jinkirin da aka samu wajen biyan su albashi da alawus-alawus ya sanya su cin bashi.

Kuɗin fara aikin da akan bai wa ƴan majalisar, tamkar na al’ada ne da ake ware musu domin kamawa da gyara muhalli, baya ga kuɗin alawus na sufuri.

Kimanin kashi 70 cikin ɗari na ƴan majalisar dokokin tarayyar ta 10 sabbi ne.

Sau da dama al’ummar Najeriya na sukar ƴan majalisunsu, musamman kasancewar sun yi amannar ana biyan su kuɗaɗe fiye da ƙima.

Kuma majalisar ta kasa wallafa yawan kuɗaɗen da ake ware mata tun daga shekara ta 2017.