Dan wasan gaba na Sifaniya Ansu Fati ya kammala ulla yarjejeniyar zaman aro na tsawon kaka ɗaya zuwa ƙungiyar Brighton Hove and Albion daga Barcelona.
Fati ya rasa gurbinsa a Barcelona, wadda ke buƙatar samar da sarari a cikin tawagarta don ɗaukar dan wasan baya na Manchester City Joao Cancelo a matsayin aro.
Yarjejeniyar Brighton na dan wasan mai shekaru 20 bai hada da wajibcin siya ba.
An kuma danganta Tottenham da Fati amma an fahimci cewa ɗan wasan ya fi sha'awar salon wasan Brighton a ƙarƙashin koci Roberto de Zerbi.
Dan wasan, wanda aka haifa a Guinea-Bissau amma ta zaɓi ya wakilci Sifaniya kuma ya kasance cikin tawagarta a gasar cin kofin duniya a bara, ya rattaba hannu a sabuwar yarjejeniya da Barcelona a shekara ta 2021 don ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa 2027.