A karo na biyu kungiyar Brighton ta ki amincewa da tayin da Arsenal ta gabatar mata kan dan kwallon tsakiya na Ecuador Moises Caicedo.
Ana tunanin a wannan karon Arsenal na shirin bayar da fan miliyan 70 domin dauko dan kwallon.
Sai dai Brighton ta ce dan wasan ba na sayarwa ba ne.
A makon da ya gabata Arsenal da Chelsea duk sun nuna sha'awar sayen dan kwallon amma aka ƙi sallama musu.
Caicedo ya shaida wa Brighton a cikin wata budaddiyar wasika cewa yana son barin kungiyar kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo a ranar Talata.
Ba a saka dan kwallon a wasan da Brighton ta doke Liverpool da ci biyu da daya a gasar cin kofin FA a ranar Lahadi ba.
Kocin kungiyar Roberto de Zerbi ya ce yana son ya kammala kakar wasa ta bana tare da Caicedo a kulob din.
Caicedo ya buga wa Brighton wasa 26 a gasar Firemiya ta Ingila inda ya zura kwallo biyu.