Koci, Robert De Zerbi ya ce yana tattaunawa da Brighton kan batun tsawaita kwantiraginsa a kungiyar.
De Zerbi, wanda ya maye gurbin Graham Potter a Satumbar 2022, ya kai kungiyar mataki na shida a kakar da ta wuce da zuwa gasar zakarun Turai karon farko.
Brighton tana mataki na takwas a Premier Lerague, ta kuma kai zagaye na biyu a Europa League.
''A kullum ina cike da farin ciki da jin dadin gudanar da aikin a Brighton,'' kamar yadda kociyan mai shekara 44 ya fada, wanda yake da sauran yarjejeniya zuwa karshen 2026.
''Ina da gagarumar alaka da 'yan wasa da kungiyar da shugaba, Tony dasauran jami'ai da kowa da kowa a Brighton.
Rawar da De Zerbi yake takawa a Brighton ya sa ake ta alakanta kociyan da cewar zai koma wasu manyan kungiyoyin Turai.
Sai dai tsohon kociyan Sassuolo da Shakhtar Donetsk ya ce ba shi da wani burin barin Brighton a nan kusa.