BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: BBC

Buhari ya ce yana takaici kan zarge-zargen da Gwamnan Benue yake yi masa

Shugaba Muhammadu Buhari Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeirya Muhammadu Buhari ya ce abin takaici ne irin yadda gwamnan jihar Benue Samuel Ortom yake zarginsa da aikata wasu laifuka.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da ywunsa Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ranar Juma'a da safe.

Ya mika jajensa ga al'ummar jihar ta Benue wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai musu a baya bayan nan.

Rahotanni sun ambato Gwamna Ortom yana zargin Shugaba Buhari da mara wa makiyaya baya a kashe-kashen da yake cea sun yi a jihar ta Benue.

Sai dai shugaban kasa ya kara da cewa babu kamshin gaskiya a zarge-zargen yana mai cewa "babu wata gwamnatin da take da hankali da za ta ji dadin irin wadannan kashe-kashe na sojoji da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da ke zaune a sansanonn 'yan gudun hijira."

Shugaba Buhari "ya bayyana takaicinsa da bakin cikin jin Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue yana yin jerin zarge-zarge a kansa da gwamnatinsa sakamakon hare-haren da aka kai a jhar a kwanakin baya," in ji Malam Garba Shehu.

Shugaban kasar ya bukaci hadin gwiwa a matakai daban-daban domin shawo kan kashe-kashe da kuma rikice-rikicen da ake yi a kasar.

"Shugaba Buhari yana matukar jin zafin rikice-rikicen da ake yi ba wai kawai a jihar Benue har ma sauran sassan kasar kuma yana tsammanin jami'an tsaro za su shiga kowanne lungu da sako na kasar domin kama wadanda suke aikata wadannan laifuka da kuma gurfanar da su a gaban kuliya," in ji Malam Garba Shehu.

Ya yi kira ga gwamnan jihar ya bai wa gwamnatin tarayya hadin kai domin shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar jihar.