BBC Hausa of Wednesday, 14 April 2021

Source: BBC

Burkina Faso: An samu Blaise Compaoré da laifin kisan Thomas Sankara

An kashe Kyaftin Thomas Sankara ranar 15 ga watan Oktoban 1987 An kashe Kyaftin Thomas Sankara ranar 15 ga watan Oktoban 1987

An samu tsohon shugaban Burkina Faso Blaise Compaoré da laifi a kashe Kyaftin Thomas Sankara ranar 15 ga watan Oktoban 1987, kamar yadda kotun soji ta Burkina Faso ta bayyana a ranar Talata.

Kotun soji ta kasar ta kama Compaoré da laifin "kai hari kan tsaron ƙasa, da hannu a kisan kai da kuma ɓoye gawarwaki" a shari'ar kisan tsohon shugaban ƙasar Thomas Sankara.

A watan Oktoban 2014 ne aka hamɓarar da Mista Compaoré kuma tun a wancan lokacin yake samun mafaka a Ivory Coast tun bayan tserewarsa.

A watan Janairu ne, kotun soji da ke Ouagadougou ta fara tabbatar da tuhume-tuhumen ƙararrakin mutum 20 da ake tuhuma da hannu a kisan Kyaftin Sankara.

Bayan kammala wadannan shari'o'i ne, waɗanda tsohon Shugaba Compaoré bai halarta ba, aka yanke hukuncin samunsa da laifin.

Kazalika an samu Gilbert Diendéré, wani na hannun daman Mista Compaoré da laifi a kisan kan yayin shari'ar, wanda aka yanke masa hukuncin zaman yari na shekara 20 sakamakon juyin mulkin 2015, kamar yadda wani rahoto na Ma'aikatar Shari'a ya ce.

Sannan an tsara cewa wasu mutum 12 za su bayyana a gaban kotunan Burkina kan laifuka masu alaƙa da shari'ar kisan.

An shigar da ƙarar su ne kan "kai hari kan tsaron ƙasa da kisan kai da yin jabu wasu takardun gwamnati da ɓoye gawarwaki da sauran su.

An kashe Thomas Sankara mai shekara 37, kuma jagoran juyin juya halin Burkina Faso ne a 1987 tare da wasu na hannun damansa 12 a wani juyin mulkin da ya yi sanadin zaman Blaise Compaoré shugaban ƙasar.

Daga baya shi ma Mista Compaoré aka hamɓarar da shi a watan Oktoban 2014, bayan shafe shekara 27 yana mulki.

A shekarar 2015 ne aka sake waiwayar shari'ar kisan Sankara.

A watan Mayun 2015, gwamnatin Burkina Faso ta haƙo gawar Sankara da ta abokansa 12 a gaban dangi da lauyoyi.

Binciken ƙwa-ƙwaf ɗin da aka yi ya gano cewa an yi kaca-kaca da jikinsa da harsasai kafin a binne shi a maƙabartar Ouagadougou.