A dai-dai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubale wajen aika kuɗi ta intanet da kuma amfani da na'urar cirar kuɗi ta POS, babban bankin kasar - CBN ya musanta bayanan da ake yada wa cewar ya bayar da umurnin katse hanyoyin tura kuɗi ta intanet a lokacin zaben da za a yi a karshen mako.
Labarin ƙaryar ya jefa fargaba a zukatan ƴan ƙasar har ta kai mutane sun fara rige-rigen zuwa kasuwanni domin tanadar abubuwan buƙata kamar abinci da man fetur domin ajiye su a gida har zuwa lokacin zaɓe da kuma bayansa.
Labarin ƙaryar da ya karaɗe ko ina musamman a manhajar Whatsapp.
A ranar Laraba ne dai CBN ya fito ya ƙaryata rahotannin da ake ta yaɗawa ba tare da yin ƙarin haske kan batun.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, CBN din ya ce babu gaskiya a labarin katse intanet kuma ba daga wurinsa sanarwar ta fito ba.
Batun sauya takardun kuɗi a Najeriya ya janyo cece-kuce a ɓangarori da dama tun bayan fara aiwatar da tsarin a Disambar 2022.
Lamarin dai ya sa an yi ta samun bayanai na ƙarya kan tsarin sakamakon rashin fitowar babban bankin Najeriya, CBN ya yi wa ƴan ƙasar bayani dalla-dalla game da manufarsa ta bijiro da shi.
Rarrabuwar kan da aka samu kan batun saka wa'adin mayar da tsofaffin takardun kuɗi zuwa ga batun ci gaba da amfani da su da kuma bayanan da aka riƙa samu daga bankuna sun jefa jama'ar ƙasar cikin fargaba da kuma rashin sanin alƙiblar da za su bi.
Daga cikin irin waɗannan bayanai masu janyo ruɗani da aka yi ta yaɗawa a baya-bayan nan akwai wanda ke cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1000 har zuwa 1 ga watan Mayun 2023.
Bankuna sun mayar da martani kan batun...
Ƙungiyar Manajojin Harkokin Kasuwanci na Bankuna (ACAMB) ta yi tsokaci kan batun.
Cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce babu ƙanshin gaskiya kan labaran da ake yaɗawa cewa bankuna za su rufe hanyoyin aika kuɗi ta intanet daga ranar Alhamis har zuwa bayan zaɓe.
“ACAMB na son karyata labaran ƙaryar tare da bai wa ƴan Najeriya tabbaci cewa babu ƙanshin gaskiya a labaran da mutane ke yaɗawa.
“Har zuwa wannan lokaci, babu wani bankin kasuwanci ko cibiyar hada-hadar kuɗi da ta samu wannan umarnin daga CBN cewa su rufe rassansu ko kuma su katse hanyoyin aika kuɗi ta intanet saboda zaɓe," in ji Sanarwar.
Ya bai wa abokanan hulɗar bankuna tabbacin cewa bankuna za su ci gaba da aiki "kafin zaɓe da ranar zaɓe da kuma bayan zaɓe."
Ya kuma ce bankuna sun tanadi matakan inganta ayyukansu ga abokanan hulɗarsu a lokacin zaɓen.
Yadda tirka-tirkar sauya fasalin kudin ta samo asali
Tun bayan da CBN ya sauya fasalin takardun naira saboda abin da ya kira magance matsalar tsaro da samun damar mayar da kuɗi bankunan ƙasar, babban bankin da farko, ya gindaya ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin.
CBN ya buƙaci mutane su mayar da tsofaffin takardun N200 da N500 da N1,000 zuwa bankunan kasuwanci domin a sauya musu da sababbin takardun kuɗin da aka sauyawa fasali tare da ƙayyade yawan kuɗaɗen da mutum zai iya cira.
CBN daga bisani ya kara tsawaita wa'adin zuwa 10 ga watan Fabrairu bayan da mutane da dama suka fuskanci kalubale wajen cirar kuɗi.
Batun dai ya dangana zuwa kotun ƙoli wadda ta ba da umarnin CBN ya dakata da ƙudirinsa kan daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi.
Wasu gwamnonin jihohin ƙasar ne suka shigar da ƙara ranar 3 ga watan Fabrairu inda suka buƙaci kotun ƙolin ta dakatar da CBN game da wa'adin daina amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar.
Kotun ta zauna ranar 22 ga watan Fabrairu - kwana uku kafin zaɓen shugaban ƙasar inda kuma ta ɗage sauraron ƙarar har sai ranar uku ga watan Maris, 2023.