BBC Hausa of Tuesday, 12 September 2023

Source: BBC

Champions League: Arsenal ta sanar da 'yan wasanta

Kocin Arsenal Mikel Arteta Kocin Arsenal Mikel Arteta

Arsenal ta sanar da 'yan wasa 25 da za su buga mata gasar Champions League kakar 2023/24.

Kamar yadda Uefa ta umarta za su ƙunshi rukunin farko na 'yan ƙwallo 25 da za su haɗar da masu tsaron raga.

Dole ne 'yan wasan su kasance waɗanda ke ƙungiyar tsawon kaka uku ko kuma waɗanda suka yi wata 36, masu shekara tsakanin daga 15 zuwa 21.

Ƙungiyar za ta iya sauya sunan ɗan ƙwallo, kafin buga karawar zagaye na biyu da za a fara cikin watan Fabrairun 2024.

A lokacin, an bai wa ƙungiyar ta sauya 'yan wasa uku waɗanda ko dai suka ji rauni ko sabbi da ta ɗauka, amma dai su zama 25, waɗanda za su ci gaba da gasar.

Arsenal, wadda daga baya za ta sanar da rukunin 'yan ƙwallo na biyu tana da damar sanar da masu tsaron raga uku da za su fara yi mata wasannin cikin rukuni.

Arsenal tana rukuni na biyu da ya hada da Sevilla da PSV Eindhoven da kuma RC Lens.

Gunners wadda ba ta taɓa daukar Champions League ba, za ta fara wasan cikin rukuni ranar 20 ga watan Satumba, inda za ta karɓi baƙuncin PSV Eidhoven.

A kuma ranar Sevilla da RC Lens za su kece-raini a tsakaninsu.

Sunayen rukunin farko:

Masu tsaron raga: Aaron Ramsdale, David Raya da kuma James Hillson

Masu tsaron baya: Cedric, Lino Sousa, Takehiro Tomiyasu, Oleksandr Zinchenko, Ben White, Gabriel, Jakub Kiwior da kuma William Saliba

Masu buga tsakiya: Mohamed Elneny, Jorginho, Thomas Partey, Declan Rice, Martin Odegaard, Kai Havertz, Fabio Vieira da kuma Emile Smith Rowe

Masu cin kwallaye: Leandro Trossard, Bukayo Saka, Gabriel Martinelli, Reiss Nelson, Eddie Nketiah da kuma Gabriel Jesus