Chelsea ta cimma yarjejeniyar daukar mai tsaron baya, Axel Disasi daga Monaco kan fam miliyan 38.57.
Disasi, mai shekara 25, dan kwallon tawagar Faransa zai bai wa Chelsea zabin buga gurbin tsare baya daga gefe ko daga tsakiya, bayan da Wesley Fofana ke jinya.
Fofana zai yi jinya mai tsawo, bayan da likitoci suka yi masa tiyata.
Haka shima Benoit Badiashile na jinya, wanda sai an fara gasar Premier League zai murmure.
Kungiyar Brighton na son daukar 'yan kwallon Chelsea masu tsaron baya da suka hada da Thiago Silva ko Trevoh Chalobah ko kuma Levi Colwill.
Disasi ya buga wa Monaco wasa 118 tun bayan da ya koma kungiyar daga Reims a Agustan 2020.
Ya buga wa Faransa karawa hudu, wanda ya fara taka leda a gasar cin kofin duniya da Tunisia a cikin watan Disamba.
Disasi shine na uku da Chelsea ta saya a bana, bayan Nicolas Jackson da kuma Christopher Nkunku zuwa Stamford Bridge.
Haka kuma kungiyar Stamford Bridge na son sayen dan wasan Rennes, Lesley Ugochukwu kan fam miliyan 23.2, wanda za ta bayar da aronsa ga Strasbourg.
Tuni dai Brighton ta yi watsi karo uku da Chelsea ta taya mai tsaron bayan, dan kasar Ecuador, Moises Caicedo.
Sabon koci, Mauricio Pochettino na kokarin ganin ya kai Chelsea kan ganiya, bayan da ya maye gurbin Frank Lampard.
Tuni Chelsea ta sayar da wasu 'yan wasan da suka hada a bana da suka hada da Mateo Kovacic da Edouard Mendy da Kalidou Koulibaly, da kuma N'Golo Kante.
Sauran sun hada Mason Mount da Kai Havertz da Christian Pulisic da Ruben Loftus-Cheek da Ethan Ampadu da Pierre Emerick-Aubameyang da kuma Cesar Azpiliceuta.