BBC Hausa of Friday, 14 July 2023

Source: BBC

Chelsea ta kakkaɓe manyan 'yan wasanta su goma

Mauricio Pochettino Mauricio Pochettino

Chelsea ta raba gari da waɗansu manyan 'yan wasanta a wannan bazarar abin da ke nuna cewa sabobbin fuskoki za a gani a ƙungiyar a kakar wasa mai zuwa.

Waɗanda suka tafi sun haɗa da Kai Havertz wanda ya koma Arsenal, sai kuma Mateo Kovacic wanda ya haɗe da Manchester City a yayin da shi kuma Mason Mount ya ƙulla yarjejeniya da Manchester United.

Shi kuma kyaftin din ƙungiyar Cesar Azpilicueta ya koma Atletico Madrid ne sai Ruben Loftus-Cheek da ya koma AC Milan a yayin da David Datro Fofana ya tafi Union Berlin a matsayin aro.

Akwai kuma wasu uku da suka koma Saudiyya domin murza leda watau Kalidou Koulibaly da ya koma Al-Hilal sai Edouard Mendy wanda ya koma Al-Ahli a yayin da N'Golo Kante ya koma Al-Ittihad.

Ɗan ƙwallon Amurka, Christian Pulisic shi kuma ya bar Chelsea ne zuwa AC Milan.

Pulisic ya buga wasa 145 a Chelsea inda ya ci ƙwallo 26.

Akwai kuma waɗansu 'yan wasan da ake tunanin za su tafi kafin a rufe kasuwar musayar 'yan ƙwallo kamar su Romelu Lukaku da Pierre-Emerick Aubameyang da kuma Hakim Ziyech.