BBC Hausa of Wednesday, 21 June 2023

Source: BBC

Chelsea ta ki sallama tayi na biyu da Man United ta yi wa Mount

Mason Mount Mason Mount

Manchester United ta kara yin tayi na biyu, domin sayen dan wasan Chelsea, Mason Mount kan fam miliyan 50.

Mount, mai shekara 24, yana cikin 'yan wasan da Erik ten Hag ke son dauka don karfafa United, wadda za ta buga Champions League a kaka mai zuwa.

Chelsea ta kashe fam miliyan 600 kan fara kakar bana, saboda haka ya zama wajibi ta sayar da wasu 'yan wasan don bin dokar kashe kudi daidai samu, wato Financial Fair Play.

Ana hasashen cewar Chelsea na son sayar da Mount kan fam miliyan 70.

Mount, wanda ya ci kwallo 33 a wasa 195 tun bayan da ya koma Chelsea, ya sha jinya a kakar da ta wuce.

Chelsea ta kare a mataki na 12 a teburin Premier League - kaka mafi muni da kungiyar ta fuskanta tun bayan kaka 25 da ta wuce.

Ya lashe Champions League a Chelsea a 2021 a lokacin da Manchester City ta yi rashin nasara da ci 1-0.

Ya kuma dauki Fifa Club World Cup da Uefa Super Cup a dai kungiyar ta Stamford Bridge.

Ya buga wa tawagar Ingila karawa 36 da cin kwallo biyar, yana cikin 'yan kwallon Gareth Bale da suka buga gasar kofin duniya a Qatar a 2022.