Chelsea na duba yiwuwar daukar dan wasan Manchester United mai shekara 30 Harry Maguire, yayin da dan bayan Chelsea dan kasar Faransa Wesley Fofana mai shekara 22 ke doguwar jinya bayan an yi masa tiyata. . (90 Min)
Newcastle za ta kammala yarjejeniya da dan wasan Leicester City kuma dan wasan gefe na Ingila Harvey Barnes nan da kwanaki masu zuwa, sannan zuwan dan wasan mai shekara 25 na nufin dan wasan gaban Faransa Allan Saint-Maximin zai bar kungiyar. . (Mail)
Al- Ahli na son Saint-Maximin inda ta yi wa Newscastle tayin bayar da kudi yuro miliyan 25 kan dan wasan. (L'Equipe - in French)
Kungiyar kwallon kafa ta Saudiya A-Hilal na sha’awar dan wasan Liverpool Luis Diaz, to amma ba lallai ba ne Liverpool din ta amince da yuro miliyan 50 da aka mata tayi. (Record - in Portuguese)
Shugaban kungiyar Paris St-Germain Nasser Al-Khelaifi, ya ga Kylian Mbabbe a harabar wajen horar da ‘yan wasan kungiyar a jiya Talata, to amma sai ya yanke shawarar ƙin haduwa da shi yayin da rashin fahimtar juna tsakanin kungiyar da kuma dan wasan na Faransa ke karuwa. (Sky Sports)
Aston Villa ta kara taya dan wasan Bayer Leverkusen kuma dan Faransa Moussa Diaby a kan kudi fam miliyan 42 da miliyan tara. (Athletic - subscription required)
Ita kuwa Manchester United za ta taya dan gaban Atalanta da Denmark Rasmus Hoilund, mai shekara 20, to amma idan har kungiyar Italiya ta ki amincewa da tayin da aka yi mata, to Manchester United din za ta karkata akalarta ga dan gaban Eintracht Frankfurt Randal Kolom ai shekara 24. (ESPN)
Marseille ta shirya tattauna da Chelsea kan Pierre-Emerick Aubameyang, a kan yarjejeniyar shekara uku da dan wasan na Gabon. (Guardian)
Chelsea na son kari kan tayin fam miliyan 40 da aka yi wa Connor Gallagher, mai shekara 23, yayin da West Ham ta matsu ta ɗauki ɗan wasan. . (Sky Sports)
Bayern Munich na son sayar da dan tsakiyar Jamus Joshua Kimmich, idan har kungiyar ta samu ta yi mai kyau kan dan wasan mai shekara 28. (Kicker - in German)
Dan bayan Manchester United Alex Telles, ya kusa koma wa kungiyar Saudiya ta Al-Nassr, yayin da dukkan kungiyoyin ke tattaunawa a kan dan wasan dan kasar Brazil mai shekara 30. (Athletic - subscription required)
Tottenham na tattaunawa da Napoli a kan yiwuwar sayar mata da dan tsakiyar Argentina Giovanni Lo Celso. (Radio Punto Nuovo via Football Italia)
Liverpool na yunkurin maye gurbin dan wasan Brazil Fabinho da ke shirin tafiyar kungiyar Al-Ittihad da ke Saudiya a kan yarjejeniyar fam miliyan 40. (Liverpool Echo)