Chelsea ta fara tattaunawa kan dauko dan wasan Benfica, na tsakiyar Argentina Enzo Fernández, mai shekara 22, kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a ranar Talata.(Telegraph - subscription required)
Tottenham ta mika yuro miliyan 25 ga Bayer Leverkusen don musayar dan wasan tsakiya na Ecuador Piero Hincapie, mai shekara 21. (Bild - in German)
Nottingham Forest na gab da rattaba hannu kan kwantiragin dauko dan wasan Newcastle United, na tsakiyar Ingila Jonjo Shelvey, mai shekara 30. (Telegraph - subscription required)
Barcelona na duba yiwuwar dauko dan wasan Atletico Madrid na gaban Portugal Joao Felix, mai shekaru 23, wanda ya ke zaman aro a Chelsea. (Sport - in Spanish)
Inter Milan na aikin hadin gwiwa da Manchester United, na baya Sweden Victor Lindelof, mai shekara 28,domin maye gurbin Milan Skriniar idan dan wasan mai shekara 27 kuma mai tsaron gidan Slovakia dya koma taka leda a Paris St-Germain. (Fabrizio Romano)
Newcastle United ta amince ta biya fam miliyan 3 domin dauko dan wasan West Ham, kuma na bayan Scotland Harrison Ashby, mai shekara 21. (Times - subscription required)
Fulham sun tattauna da Sheffield United kan dauko dan wasan tsakiya na Norway Sander Berge, duk da cewa dan wasan mai shekara 23 na da alaka da Newcastle. (90min)
Ana kuma ci gaba da tattaunawa domin dauko dan wasan tsakiya na Serbi Sasa Lukic mai shekara 26 daga Torino. (Athletic - subscription required)
Brighton hta kammala yarjejeniyar dauko dan wasan AIK na tsakiyar Sweden Yasin Ayari, mai shekara 19, kan farashin kusan fam miliyan 6. (Fabrizio Romano)