Asusun Kula da Ƙananan Yara Na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce ɗaya a cikin ko waɗanne yara huɗu a Najeriya na fuskantar cin zarafi; kuma ana cin zarafin ɗaya a cikin kowace yarinya uku a ƙasar ta hanyar lalata.
Wannan rahoto ya zo ne a Ranar Yara a Najeriya, wadda ake yi a kowace ranar 27 ga watan Mayu a kasar, domin tattaunawa kan batutuwan da suka jibanci yara da kuma taimaka musu wajen gano cewa su ne manyan gobe.
Babban jami'in Unicef a Najeriya Peter Hawkins ya shaida wa BBc cewa waɗannan alƙaluma abin damuwa ne ainun.
An samu alƙaluman ne daga wani nazari da aka yi kan wasu bayanai da Ma'aikatar Mata Ta Najeriya da Hukumar Raya Ƙasashe Ta Amurka USAID da kuma Unicef suka tattaro.
Hawkins ya ce an samu ƙaruwar cin zarafin mata a watannin Afrilu da Mayun 2020 da watannin Janairu da Fabrairun 2021.
Kuma kasancewar ba duka abubuwan da ke faruwa ne ake samun labarinsu ba, akwai fargaba ƙwarai cewa lamarin ya fi haka muni.
Unicef ta ce idan annobar cutar korona ta ci gaba da wanzuwa to akwai yiwuwar cin zarafin mata da yara ya ƙara ƙamari.
An tilasta wa yaran zama cikin wani yanayi maras daɗi a yayin kullen da aka yi inda aka ci da guminsu kuma aka ci zarafinsu.
A bara gwamnonin ƙasar 36 sun nuna damuwa kan yawaitar fyaɗe da cin zarafin mata da yara.
Unicef ta buƙaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙarfafa tsare-tsaren kai rahoton cin zarafi kuma ta riƙa hanzarta hukunta masu fyaɗe da cin zarafin ƙananan yara.
Mece ce Ranar Yara Ta Najeriya
Ana yin bikin ne duk ranar 27 ga watan Mayu a Najeriya. An fara yinsa a shekarar 1964 inda aka ayyana ranar a matsayin ranar hutu ga ƴan makarantun firamare da sakandare.
Akan shirya fareti ga yara a jihohin ƙasar daga makarantu daban-daban, wasu ma sukan yi ne a manyan dandalin da ke jihohin a gaban gwamnoni.
Wasu yaran kuma iyayensu kan fita da su filayen shaƙatawa ko na wasa domin su ji daɗin ranar.
Kuma ƙungiyoyi da hukumomin gwamnati kan fitar da rahotanni ko sakamakon wasu bincike da aka gudanar a kan muradun yara a wannan yara.
Sannan kafofin yaɗa labarai na taka rawa wajen wayar da kai kan muhimmancin ranar.
Amma kowace ƙasa ta duniya da akwai ranar da ta ware don bikin Ranar Yara - ba tare ake yi duk duniya ba.
Kazalika akwai Ranar Yara Ta Duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware da ake bikinta a ranar 20 ga watan Nuwamban wannan shekara.
Ƙasashe irin su Amurka da Birtaniya sun fi bikin tasu Ranar Yaran a wannan lokacin.