BBC Hausa of Friday, 7 July 2023

Source: BBC

Cutar mashaƙo ta ɓarke a Abuja

Hoton alama Hoton alama

Cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce an samu barkewar cutar mashako (Dphtheria) a babban birnin kasar Abuja, bayan da wani yaro mai shekara hudu ya rasu.

Cutar mai saurin yaduwa tana shafar hanci da makogaro ne ta hana numfashi daga nan kuma takan kai ga illata zuciya da kuma sanya kumburi a jikin mutum, inda yawanci take kama yara masu shekara tsakanin biyu zuwa 14.

Rahotanni sun ce yaron da cutar ta kashe ba a yi masa rigakafi ba.

A sanarwar da hukuma ta bayar a ranar Alhamis ta ce daman an samu bullar cutar a sassan kasar da dama tun a shekarar da ta gabata.

Zuwa yanzu an samu mutuwar mutum akalla 80 daga cikin mutum kusan 800 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kusan jihohi takwas na kasar.

Jihohin da aka samu bullar cutar sun hada da Lagos wadda ta fi yawan jama’a da Kano wadda take bi mata da kuma Abuja babban birnin kasar, zuwa karshen watan Yuni na wannan shekara.

Cut ace da take daga cikin wadanda ake yi wa rigakafin da galibi ake yi wa yara, amma duk da haka yawancin wadanda ta kama su kusan 800 ba a yi musu rigakafi ba kamar yadda bayanai suka nuna.

Hukumomin lafiya a Najeriyar sun bukaci jama’a su sanya ido sosai tare da kai rahoton duk wanda aka ga alamun cutar a tattare da shi domin daukar matakin da ya dace na gaggawa.

Hukumar ta ce tana yin aiki da hadin gwiwar jami’an lafiya domin yaki da bazuwar cutar a kasar ta Najeriya wadda it ace mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka.

Alamomin cutar na fara bayyana a jiki ne cikin kwanaki biyu zuwa biyar.

Ga dai wasu daga cikin alamomin cutar:

  • Tari


  • Zazzabi mai zafi


  • Rashin cin abinci


  • Kumburin cikin baki.


  • Numfashi sama-sama


  • Yoyon hanci


  • Gajiya


  • Hanyoyin kauce wa kamuwa da cutar mashaƙo

    Likitoci sun ce hanya daya ta kaucewa kamuwa da cutar mashako ga manya da kananan yara ita ce yin allura saboda za ta kashe kwayoyin cutar da ke jikin mutum.

    Yana da muhimmanci a wayar da kan al’umma wajen yi wa yara alluran rigakafi domin hakan zai iya magance ba wai mashako kadai ba har da cutar sarkewar hakora da kyanda da sauransu.