BBC Hausa of Wednesday, 9 August 2023

Source: BBC

Da gaske ne mayaƙan Wagner sun isa Nijar?

Tutar Nijar Tutar Nijar

Jim kaɗan bayan juyin mulki a Njar, mutane sun yi ta yaɗa labaran ƙarya a intanet, abin da ke ƙara ta'azzara lamurra a ƙasar da ke yammacin Afirka.

Mun duba wasu daga cikin labaran da aka fi yaɗawa.

Tsofaffin hotunan da aka jirkita sun nuna mayaƙan Wagner na hallara

Amurka ta ce mayaƙan ƙungiyar Wagner na "amfani da damar" zaman ɗarɗar da ake yi a Nijar - amma zuwa yanzu babu wata hujja da ke nuna akwai mayaƙan ƙungiyar a ƙasar.

Mayaƙan Wagner na aiki a ƙasashen Afirka kamar Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Wani bidiyo da ake yaɗawa ya yi iƙirarin cewa na sojojin Rasha ne ke sauka a birnin Yamai tare da kalaman cewa "tuni Wagner ta fara shiga birnin".

Jirgin da aka nuna a bidiyon bai yi kama da IL 76 ba na sojan saman Rasha, amma bidiyon tsoho ne.

Binciken da sashen BBC Verify ya yi ya nuna cewa an fara saka bidiyon a dandalin Youtuba tun a 2006, kuma jirgin na sauka ne a birnin Khartoum na Sudan.

Gine-ginen da aka gani a bidiyon sun yi kama da waɗanda suka zagaye filin jirgi na Khartoum.

Wani bidiyon da aka kalla fiye da sau 500,000 a TikTok - ya nuna mayaƙan Wagner a Afirka cikin tsohon bidiyon a matsayin hujja ta farko ƙarara da ke nuna zuwansu Nijar.

An ciro shi ne daga rahoton kafar talabijin ta France 24 a watan Janairun da ya gabata, inda yake magana kan aikin Wagner a Mali maimakon Nijar.

AN gurɓata bidiyon ne don cire rubutun da ke kan majigi mai fayyace cewa Mali ake nufi.

Haka nan, an yaɗa wani tsohon hoton Wagner a Ukraine da ikirarin cewa suna yunƙurin tura mayaƙa Nijar.

Labaran ƙarya game da haramta safarar makamashin uranium

Wani iƙirarin da aka yaɗa bayan juyin m,ulkin shi ne cewa sojojin mulkin sun haramta fitar da makamashin uranium zuwa Faransa.

Wasu saƙonnin kamar wannan da ke sama, ya ƙunshi akasari alƙaluma na gaskiya game da yawan uranium da ake fitarwa zuwa Faransa da Tarayyar Turai, amma babu wata hujja cewa sojojin sun haramta yin hakan.

Kamfanin Faransa da ke aikin haƙar uranium a Nijar, Orano Group, ya ce ya ci gaba da ayyuka a yankunan Arlit da Akokan, da kuma hedikwatarsa da ke birnin Yamai.

Sojojin Nijar ba su tsare 'yan ƙasar waje

Yayin da wasu ƙasashen Turai suka fara kwashe mutanensu daga Nijar, wasu iƙirari marasa hujja sun ɓulla cewa sojoji sun ba da umarnin fara tsare Turawan.

Suka ce an yi hakan ne wa don a matsa wa ƙasashen su janye sojojinsu daga Nijar.

Da alama an alaƙanta iƙirarin ne da kiran da ƙungiyar M62 ta yi, wadda ke goyon bayan sojin da kuma ƙin jinin Faransa, cewa a tsare Turawa har sai an janye dukkan dakarun ƙasashen waje.

Sai dai kuma ƙungiyar ba ta magana da yawun gwamnati.

Jagoran juyin mulki Janar Abdourahmane Tchiani ya faɗa a makon da ya gabata cewa 'yan Faransa ba su da wata fargaba "kuma ba a taɓa yi musu wata barazana ba".

Akwai sojojin Faransa da na Amurka a Nijar, kuma ba su bar ƙasar ba har yanzu suna nan.

Aljeriya ba ta ce tana goyon bayan sojojin Nijar ba

Kazalika, an yi ta yaɗa cewa Aljeriya mai maƙwabtaka da Nijar za ta taimaka wa sojojin mulkin ƙasar idan sojojin ƙasar waje suka kai musu hari.

"Aljeriya ba za ta rungume hannayenta ba yayin da ake kai wa maƙwabciyarta hari," a cewar wani ma'abocin Twitter yana mai alaƙanta shi da kafofin labarai na Aljeriya.

Ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, Ecowas, ta yi barazanar saka hannun (ciki har da ƙarfin soja) idan ba a mayar da Shugaba Bazoum kan mulki ba.

Sai dai Mali da Burkina Faso - mambobin Ecowas da sojoji ke mulka - sun ce za su goyi bayan 'yan uwansu na Nijar idan aka kai musu hari.

Aljeriya ta ce tana adawa da kai wa Nijar hari, amma abu mafi muhimmanci, ba ta ce za ta taimaka wa shugabannin juyin mulkin ba idan aka kai musu harin.

Mun duba shafin Intel Kirby, wanda akasarin masu yaɗa iƙirarin ke alaƙantawa da rahoton, ya wallafa saƙo a ranar 30 ga watan Yuli cewa "Aljeriya ba za ta rungume hannu ba yayin da ake kai wa maƙwabciyarta hari," amma ya ce wannan ra'ayinsa ne game da abin da zai iya faruwa - ba sanarwa ba ce daga gwamnati.

Ƙarin rahoto daga Jake Horton da Paul Brown.