BBC Hausa of Friday, 14 July 2023

Source: BBC

'Da idona na ga ana jibge gawarwaki a ƙatoton kabari a Sudan'

Hoton alama Hoton alama

Maalim ya shiga tsananin damuwa saboda abin da idonsa ya gane masa a yankin Kudancin Darfur na asar Sudan gabanin tsallakawar da ya yi zuwa Chadi.

Ya shaida wa wakilin BBC cewar: "Idan abokan aikina suka san cewa na nuna maka waannan hotuna da bidiyo ko ma suka san cewa na ɗauke su, to na zama gawa."

Ya faɗi hakan ne a lokacin da yake ciro wayarsa domin nuno wasu hotuna marasa daɗin gani na gawarwaki barbaje a birnin El Geneina.

Mun sauya sunansa domin kare shi.

Kafin ya bar ƙasarsa, yana cikin mutanen da aka ɗora wa alhakin kwashe gawarwaki daga kan tituna da binne su a mayan ƙaburbura.

Sudan ta faɗa cikin rikici bayan da faɗa ya ɓarke tsakanin dakarun soji biyu masu adawa da juna.

Yaƙin, tsakanin dakarun RSF da na gwamnati ya ɓarke ne a watan Afrilu, inda yaƙin ya ƙazance a Darfur, yankin da dakarun RSF ke da ƙarfi.

Gargaɗi: Wannan rahoto na ɗauke da hotuna masu tayar da hankali

Hotunan na nuna gomman gawarwaki, wasu daga cikin su an rufe da bargo ko zannuwa, wasu daga cikin su sun kunbura inda suka fara ruɓewa.

Maalim ya kuma nuna hotunan gine-ginen wasu ƙungiyoyin bayar da agaji waɗanda aka farfasa aka kwashe kayan da ke ciki.

Ya faɗa wa wakilin BBC cewa: "Na shiga damuwa. Ina ganin cewa waɗannan mutane sun mace a lokacin da suke cike da tsoro. Yawancinsu gawarwakinsu sun shafe mako guda yashe a kan titi."

Za a iya cewa hoton mafi rashin daɗin gani da ya nuna shi ne wanda ya ɗauka yana ɓoye a jeji, inda aka nuno yadda wata babbar mota take jibge gawarwaki a wani wagegen rami.

Maalim ya ce: "Mun tafi daji ne da nufin binne gawarwakin. To amma mayaƙan RSF suka hana mu. Ƙungiyar ta umarci direban motar ya jibge su a wani rami."

Ya ƙara da cewa mayaƙan sun umarce su da su bar wurin bayan jibge gawarwakin.

Ya ce: "Ya kamata a ce an yi musu jana'iza daidai da tsari na Musulunci. Ya kamata a ce mun yi musu sallah da addu'a. To amma sai RSF ta sanya aka watsar da su kamar shara."

Babu wanda ya san ko gawarwakin su wane ne ko kuma ƴan uwansu. Sai dai mutane da yawa waɗanda ke samun mafaka a Chadi sun shaida mana cewa RSF sun rinƙa neman matasa da yara maza a kudancin Darfur, suna zaƙulo su suna kashewa.

Mutanen sun ce ana kai farmakin ne kan ƙabilun da ba Larabawa ba. Sun bayyana yadda akan tsayar da su a cibiyoyin bincike na dakarun RSF ana tambayarsu ƙabilarsu.

Sun ce sukan ji tsoron bayyana kansu a matsayin ƴan ƙabilar Masalit saboda gudun kada a kashe su.

BBC ta nemi jin ta bakin RSF game da zarge-zargen amma ta ƙi cewa uffan. Amma a a farkon makon nan RSF ta musanta aiwatar da kashe-kashe kan ƙabilar Masalit a watan Mayu.

Bayanin Maalim ya zo daidai da bayanin Majalisar Ɗinkin Duniya da aka wallafa a ranar 13 ga watan Yuli, wanda ya ce an umarci wasu miutane su zubar da gawarwakin ƴan ƙabilar Masalit guda 87 da wasu ma na daban a ƙatoton rami, waɗanda dakarun RSF suka kashe a yammacin Darfur.

Bayanin hotunan da ke cikin wayar Maalim na nuna cewa an ɗauke su ne tsakanin ranakun 20 da 21 ga watan Yuni, daidai da ranakun da rahoton MDD ya ambata.

Kamar yadda rahoton na MDD ya bayyana, Maalim ya shaida mana cewa an jibge gawarwakin ne a wani fili a yankin da ake kira al-Turab al-Ahmar, yamma da birnin El Geneina, kusa da wani sansanin ƴan sanda.

Bayanin MDD ya ce wasu daga cikin mutanen sun mutu ne sanadiyyar rashin samun kulawa bayan samun rauni.

A ɗaya daga cikin bidiyon da Maalim ya nuna akwai wani mutum mai rai a cikin tarin gawarwaki. Ƙudaje na bin lebɓan mutumin waɗanda suka tsattsage yayin da yake ƙoƙarin yin magana.

Maalim ya ce mutumin ya kwashe kwana takwas yashe a wurin yana fama da raunukan da ya samu daga harbin bindiga.

Ba mu abin da ya faru ga mutumin ba.

Maalim ya shaida wa BBC cewar ya ɗauki hotunan ne saboda yana son ajiye bayanan abubuwan da suka faru a garinsu.

Sai dai daga baya ya fahimci cewa ransa na cikin haɗari idan ya ci gaba da zama a garin.

Ya ce "Na ji tsoro, kasancewar a lokuta da dama sun rinƙa bincike don gano masu waya a lokacin da suke kwashe gawarwakin."

Larabawan Darfur da baƙaƙen fata ƴan asalin Afirka sun daɗe suna zaman doya da manja - an samu ɓarkewar rikici mafi muni ne a yankin shekaru 20 da suka wuce a lokacin da ƙabilun da ba Larabawa ba suka ɗauki makamai bayan sun zargi gwamnati da tsangwamarsu.

RSF ta samo asali ne daga dakarun Janjaweed ta Larabawa, wadda ta murƙushe yunƙurin ƙabilun yankin, inda ta kashe dubban ɗaruruwan mutane na ƙananan ƙabilu.

An zargi ƙungiyar da munanan laifukan yaƙi da kisan ƙananan ƙabilu, wanda aka bayyana a matsayin kisan kiyashi na farko da aka samu a ƙarni na 21.

Alamu na nuna cewa kashe-kashen na baya-bayan nan ana yin su ne da gangan. Akwai zarge-zargen da ke cewa RSF da sauran ƙungiyoyin Larabawa mayaƙa na far wa baƙaƙen fata, inda suke tursasa masu tserewa zuwa Chadi.

Kamar sauran dubban ƴan gudun hijira da suka tsero daga Darfur, Maalin bai baro wani abu da zai sanya shi ya koma ba.

An ƙone gidan iyalansa ƙurmus tare da kwashe duk abin da suka mallaka. Sannan babban abin baƙin ciki shi ne koda ya koma ba zai iske ƴan uwa da abokan arziƙi ba.