BBC Hausa of Monday, 12 June 2023

Source: BBC

Dabaru bakwai na rage yawan shan mai a mota

Hoton alama Hoton alama

Masana harkokin sufuri a Najeriya sun fara bayar da shawarwari ga direbobi da masu amfani da ababen hawa kan matakan da za su bi domin rage yawan man fetur din da motocinsu ke sha.

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin ƙasar ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa ƙaruwar farashin man a fadin ƙasar.

Masanan sun ce akwai buƙatar direbobi da masu amfani da ababen hawa su ɗauki matakin rage yawan man da motoci da sauran ababen hawansu ke sha, don kauce wa ƙarewar man da wuri.

Sulaiman Ibrahim shugaban cibiyar bincike kan harkokin sufuri ta Najeriya ya lissafa wasu hanyoyi da ya ce idan direbobi suka bi za su taimake su wajen rage yawan man fetur ɗin da motocinsu ke ƙonawa.

Tabbatar da cikar iskar tayoyi

Masanain harkokin sufurin ya ce ya kamata direba ya lura da gejin tayoyinsa, ya tabbatar da cewa iskar da ke ciki ta kai adadin gejin da aka rubuta a jikin tayarsa.

Yin hakan zai taimaka wajen rage nauyin tayoyin, abin da kuma zai taimaka wajen rage nauyin motar.

''A don haka ne nake shawartar direbobi su riƙa kula da tayoyin motarsu domin tabbatar da cewa gejinsu ya kai abin da tayoyin ke buƙata'', in ji shi.

Guje wa yawaita taka totur da birki

Sulaiman Dauda ya ce yawan taka totur da birki akai-akai na ƙara yawan man da mota ke sha.

Ya ce za ka ga wasu direbobi yanzu za su taka totur domin mota ta yi gudu ta iso wani waje da suke son isa, kuma da zarar sun isa sai su taka birki, kuma yin hakan zai sa motar ta zuƙi mai a lokaci guda.

''Misali, za ka ga direba na tafiya a kan titi kuma akwai wasu motocin a gabansa da 'yar tazarar da ba ta da yawa, amma sai su taka mota domin tarar da wadancan motoci, da zarar sun isa sai su sake taka birki. Haƙiƙa yin hakan na ƙara yawan man da mota ke zuƙa','in ji masanin.

Nauyin mota

A cewarsa nauyin mota na ƙara yawan man da za ta sha, saboda injinta zai yi nauyi.

Ya ƙara da cewa ''idan ka samu motoci biyu za su tafi waje guda, ɗaya an maƙare ta da kayan nauyi, ɗayan kuma ba ta da nauyi, to ko da sun iso wajen a lokaci daya za ka samu wadda take da nauyi ta fi shan mai''.

A don haka ne ya shawarci direbobi da su guji maƙara motocinsu da nauyi, domin tattala man fetur ɗin da motar za ta sha, musamman a wannna lokaci da man ya yi tsada sakamakon cire tallafin man fetur.

Shin kun san cewa gudu ba ya sa shan mai?

Sulaiman Dauda ya ce idan ana tafiya da mota a maleji 20 zuwa ƙasa da 60, to za ta sha mai sosai kasancewar tana giya huɗu ne wanda a cewarsa lambar giya ce mai nauyi.

Amma a cewarsa idan mota ta kai 60 zuwa 100, to ba za ta sha mai da yawa ba kasancewar tana giya lamba biyar wanda ba shi da nauyi.

Sai dai ya ce idan gudun ya zarce 100 zuwa 110, a nan ma shan man motar zai ƙaru.

A don haka ne ya shawarci direbobi cewa idan suna tafiya a kan babbar hanya lafiyayya da su zarce maleji 100, idan suna so kar motarsu ta sha mai da yawa.

Shin kunna AC na janyo shan mai?

Masanin harkokin sufurin ya ce kunna AC a mota na sa injin motar ya yi nauyi, lamarin da kuma zai taimaka wajen ƙara yawan man da motar ke zuƙa, musamman idan mutum na tafiya ƙasa da 60.

Sai dai ya ce idan mutum na gudun da ya kai 60 - 100 zuwa sama to ya iya kunna AC, sannan ya rufe gilas din motar tasa.

Sauke gilashin mota na sa shan mai

Masanin ya ce a lokacin da mota ke tafiya tana faɗa ne tsakaninta da iska, kamar tana fasa iskar ne tana ratsa ta.

To idan gilas ɗin a buɗe yake iska za ta shiga cikin motar, sannan ta yi ƙoƙarin fita ta baya, to a lokacin da ta je gilas ɗin baya a rufe, za ta riƙa turawa ne, don haka za ta riƙa jan motar baya.

''Ka ga kenan za ka riƙa jan taka mota da ƙarfi domin janta da iska ke yi, wanda kuma hakan na saka shan mai sosai'', in ji shi.

A nan sai masanin ya shawarci direbobi da su riƙa rufe gilas din motar, su riƙa kunna AC, idan tafiyar tasu ta haura 60, a nan ya ce ba za ta sha man da za ta sha idan gilas din na buɗe ba.

Kashe mota a wuraren fitilar bayar da hannu

Sulaiman Dauda ya shawarci direbobi, da su dinga kashe motarsu a wuraren tsayuwar danja matuƙar sun san cewa tsayuwar tasu za ta iya haura minti ɗaya zuwa sama.

Domin bayar da dama ga injin motar ya samu hutu.

Sai dai ya ce idan direba ya san cewa tsayuwar tasa ba za ta kai minti daya ba, to kada ya kashe motarsa, domin kuwa kunna ta ma na haifar da shan man, kasancewar sai an taka ta bayan kunna ta.