Sweden na shirin bin sahun makwabciyarta Finland wajen zama sabuwar mamba a kungiyar tsaro ta Nato, bayan da shugaban Turkiyya ya jingine kalubalantar hakan da ya sha yi a baya.
A watan Afirilun da ya gabata ne Finland ta shiga kungiyar a hukumance, lamarin da ya kara adadin mambobin kungiyar zuwa 31.
Kasashen biyu sun dade suna zama 'yan ba-ruwanmu ta fuskar soji, to amma matsayin nasu ya sauya a watan Fabarairun 2022, lokacin da Rasha ta mamayi Ukraine, yaki mafi girma a Turai tun bayan yakin duniya na biyu.
Me ya sa suka shiga ƙungiyar yanzu?
Mamayar da Vladimir Putin ke yi wa Ukraine ta girgiza zaman lafiya da aka dade ana samu a arewacin Turai, lamarin da ya sa Sweden da Finland suka razana.
Tsohon Firaministan Finland Alexander Stubb ya ce yunkurin shiga kawancen Nato da kasarsa ta yi bara ya samo asali ne daga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a shekarar da ta gabata.
Ga 'yan kasar da dama wannan ba wani bakon abu ba ne a wajensu.
Domin kuwa a shekarar 1939 Tarayyar Soviet ta mamaye kasar Finland.
Dakarun Finland sun kwashe fiye da wata uku suna kokarin kare kasarsu, duk kuwa da kashe da yawa daga cikinsu da aka yi.
A lokacin Finland ta samu nasarar kare kanta, to amma ta rasa lardin Karelia da ke gabashin kasar, wanda ya koma hannun Rasha.
Sun kauce wa mamaya, to amma sun rasa kashi 10 ciki 100 na kasarsu.
Don haka yakin da ake yi yanzu a Ukraine na tuna musu irin halin da suka shiga a lokacin mamayar rusasshiyar Rarayyar Soviet, kamar yadda Iro Sarkka wata kwararriya kan harkokin siyasa a Jami'ar Helsinki ta bayyana.
Haka kuma a 'yan shekarun baya-bayan nan ita ma Sweden tana jin cewa kamar tana cikin hatsarin mamayar.
An gano raunin sojin Sweden ne a shekarar 2013, lokacin da Rasha ta yi kokarin gwajin makamai zuwa birnin Stockholm ta amfani da jiragen yakinta, ta yadda dole sai da Sweden ta nemi taimakon Nato domin hana hakan faruwa.
A shekarar 2014, mutanen Sweden sun razana da wasu rahotonni da ke cewa jiragen ruwan karkashin teku na Rasha na yawo a tekun birnin Stockholm.
Yaya karfin sojin kasashen yake?
Kasar Finland wadda ke da yawan al’umma miliyan 5.5, tana da yawan dakarun soji da ta horas kusan 900,000, inda a kowa ce shekara take horas da sojoji akalla 21,000.
Kuma an kiyasta cewa yawan dakarun sojinta da ke iya fita filin daga ya kai 280,000.
Amma ita Sweden ba ta da yawan soji kamar Finland, domin kuwa yawan sojojinta shi ne 57,000.
To sai dai a shekarar 2018 ta dawo da horas da sojoji a kasar, shirin da ta dakatar a shekarar 2010, inda a yanzu take da dakarun kar-ta-kwana 6,000 ana kuma sa ran adadin zai kai 8,000 nan gaba.
Sweden ta rage yawan sojojinta a shekarun 1990, sannan ta sauya manufar sojinta daga kare kan iyakokinta zuwa wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya.
To amma mamayar da Rasha ta yi wa yankin Crimea a shekarar 2014 tare da bazaranar da take yi wa yankin Baltic ya tayar da Sweden a tseye domin kare kanta.
Mene ne zai sauya?
Sweden da Finland sun kasance manyan kawayen kungiyar Nato a shekarar 1994, kuma tun daga lokacin suka kasance masu taimaka wa kawancen.
Sun bayar da gudunmowa a ayyukan kungiyar tun bayan yakin cacar- baka.
A yanzu kasashen biyu za su samu kariyar tsaro daga kasashen da suka mallaki makamin nukiliya, a karkashin sadara ta 5 ta kundin dokokin Nato, wadda ta tanadi cewar, ''kai hari kan mamba daya na kungiyar, tamkar kai hari ne kan sauran kasashen kungiyar''.
Henrik Meinander wani masanin tarihi ne ya kuma ce 'al'ummar Finland sun dade suna shirin shiga Nato, tun bayan wargajewar Tarayyar Soviet.
A shekarar 1992, kasar ta sayi jiragen yaki 64 daga Amurka.
Shekara uku bayan haka ta shiga kungiyar Tarayyar Turai, tare da Sweden kuma tun daga wancan lokaci duka gwamnatocin kasashen ba su da wani buri fiye da na shiga kawancen Nato.
Mene ne hatsarin hakan?
Shugaban Rasha Vladimir Putin yayi amanna cewa bunkasar da Nato ke yi babbar barazana ce ga tsaron kasarsa, ya kuma yi ikirarin cewar hakan ne ya sanya shi kaddamar da yaki a Ukraine a 2022.
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta zargi Nato da yi wa kasashen Sweden da Finland barazana domin shiga kungiyar.
A yanzu da Sweden ta samu sahalewar Turkiyya domin shiga kawancen, Rasha ta ce za ta mayar da martani kan irin matakan da ta dauka kan Finland.
To sai dai har yanzu ba a san matakan da take shirin dauka ba.
Rasha ta ce ta girke makaman nukiliyarta da za ta iya harbawa a kowa ne lokaci a kasar Belarus, kuma za su iya kaiwa Finland da Sweden.
To sai dai tsohon firaministan Finland Alexander Stubb ya yi gargadin samun karuwar hare-haren Rasha da saba wa dokokin keta sararin samaniyar kasashen.
Me ya sa Turkiyya ta ki amince wa Sweden da Finland?
Tun da farko Turkiyya da Hungary sun nuna turjiya kan bukatar kasashen ta shiga kungiyar.
Ita dai Turkiyya ta zargi kasashen biyu da goyon bayan abin da ta kira kungiyoyin ta'addanci, ciki har da kungiyar 'yan tayar-da-kayar-bayan PKK ta Kurdawa da kungiyar Fethullah Gülen, wadda Turkiyya ta zarga da yunkurin juyin mulki a shekarar 2016.
Kurdawa su ke da kashi 15 zuwa 20 na adadin al'ummar Turkiyya, kuma hukumomin kasar sun kwashe zamunna masu yawa suna muzguna musu.
To sai da Sweden ta kasance kasar da ke bai waKurdawan mafaka, inda suka kwashe gomman shekaru suna harkokinsu a kasar.
Shugaban Turkiyya ya ce ''ta yaya kasar da ke da 'yan tayar-da-kayar-baya za ta taimaka wa Nato?
Babbar bukatarsa ita ce Sweden ta kawo karshen taimakon kudi da makamai da take bai wa masu tayar-da-kayar-baya.
A watan Yunin 2023, Sweden ta sabunta dokokin yaki da ta'addancinta, ta hanyar dakatar da kanta daga tallafa wa kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.
Kuma makonni bayan haka aka yanke wa wani Bakurde hukuncin dauri sakamakon yunkurin tallafa wa kungiyoyin ta'addanci da kudi.
To sai dai akwai wani zargi da ake yi wanda Turkiyya ta musanta, cewa babban dalilin da ya sa ta amince wa Sweden shi ne tana bukatar Amurka ta samar mata da jiragen yaki samfurin F-16.