An dade ana samun takun-saka tsakanin wasu gwamnoni jihohi da mataimakansu, inda lamarin kan munana su yi baram-baram, har ta kai ga a tsige mataimakan sakamakon sabanin da kan shiga tsakaninsu.
Duk da cewa an samu gwamman shekaru da komawar kasar ga turbar demokuradiyya, har yanzu wannan matsalar ba ta kaura ba.
Ko an `yan kwanakin nan dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamnan jihar Edo da mataimakinsa, har an fitar da shi daga cikin gidan gwamnati.
Tun komawar Najeriya ga turbar demokuradiya, wato 1999 ake samun rashin jituwa tsakanin wasu gwamnonin jihohi da mataimakansu, kuma zuwa yanzu daga cikin jihohin kasar 36, kalilan ne ba samu irin wannan zaman-tsama ko takun-sakar ba, inda wasu mataimakan a kan yi musu kora da hali, wani lokaci ma korar-kare, kasancewar ak an yi amfani da karfin iko inda suna ji suna gani ake tsige su.
Don misali, an ga irin wannan zaman-kudan a wasu lokuta a jihohin Zamfara da Ondo, da Kogi, da Abia, da Adamawa, da Bayelsa, da Ebonyi, da Plateau, da Akwa Ibom, da Bauchi, da Taraba, da Oyo, da Osun, da Enugu, da Imo, da Lagos, da Kano.
Ko zancen da ake yi ma ba wani ga maciji tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shuaibu, wanda a baya bayanan wasu kafofin sadarwa sun nuna shi ya yi cirko-cirko, an rufe masa get, an hana shi shiga gidan gwamnati.
Wasu mazauna jihar Edo sun shaidawa BBC cewa su na jin takaicin abin da ke faruwa:
“ Wannan dambarwa da ake tsakanin gwamna da mataimakinsa yana ba mu mamaki saboda tsakanin ubangida da dangida ya kamata a samu kyakyawan fahimta, sai ga shi yanzu ya kai ga tsakanin mabiyan gwamna da mabiyan mataimaki abin ba dadi,”
“ Duk inda aka ce manya biyu su na fada ina maganar jin dadi? Kuma duk abin bai wuce a kan tsayawa takara ba".
Wasu masana siyasa dai sun gano cewa wasu gwamnonin sun mai da mataimakansu safaya-taya ne, wadda sai ta-baci ake nemanta, saboda kundin tsarin mulkin Najeriya bai yi wa mataimakan gata ba da kuma wasu dalilai.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, malami a jami`ar Bayero ta Kano:
” Shi mataimakin gwamna ba shi da wani aiki sai abinda gwamna ya ba shi, wasu mataimakan gwamna za su ga ba a yi da su, idan ya yi yunkurin ya ga ya samu madafa to wannan zai tunzura gwamnan, shi yasa ma idan gwamnan ya kare wa’adinsa za ka ga akwai kiyashi, ba zai so ya bai wa mataimakinsa ba ya dora,”
„"Da ma da shi gwamnan da mataimakin gwamnan ba wai tafiya ce suke ta sabawa ba, yawancin wasu masu karfi ne a cikin jam’iyya su, za su dauko dan takara su a ba shi gwamnan domin ya samu tikitin tafiya, irin wannan za ka ga ana zaman doya da manja," in ji shi.
Masanin ya kuma yi bayani a kan tasirin ma su zuga da ke cewa mataimakan suna yin karfi har su kai yadda za su tsige gwamnan domin mataimakin gwamnan ya samu damar hawa.
MAFITA
Farfesa Kamilu Fagge ya ce ba za a rabu da matsalar dan mowa da dan bora tsakanin gwamnoni da mataimakan nasu ba idan ba a gyara wa demokuradiyyar zama ba:
"Sai tsarin mulkimu da dokokinmu sun duba sun ga yadda za a yi shi kansa mataimakin gwamnan ya samu wani aiki nasa a cikin dokokin kasa, kuma wanda zai yi takara ya zamo tun kafin ma ya yi takara gwamnan ya zabi mutun kan ra’ayin kansa”, in ji shi.
Rigimar da ake samu tsakanin wasu gwamnoni da mataimakansu, za a iya cewa ta zama ruwan dare, kuma ba jam`iyyar da ba a samu.
A kwanan nan ma an ambato shugaban jam`iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje na nuna damuwa dangane da yawaitar rikicin, lamarin da ya ce idan ta kama jam`iyyar za ta shirya taro na musamman don samun mafita.