BBC Hausa of Friday, 27 January 2023

Source: BBC

Dalilin da ya sa albasa ta fi nama tsada a Philippines

Hoton alama Hoton alama

"Babu ƙarin albasa. Kowane wurin sayar da abinci na fama da ƙarancin albasa. Kana iya ganin hakan a ko’ina.’’

A cewar alkaluman hukumomi, farashin albasa ya yi tashin gwaron zabbi a Philippines zuwa kuɗin ƙasar peso 700 kan kowane kilo.

Hakan na nufin cewa albasa ta fi nama tsada da kuma adadin kuɗin da ƙasar ke biya  a rana.

Duk da cewa farashin ya ɗan sauko cikin kwanakin nan, albasa dai sai wane-da-wane ke iya saya, a cewar Rizalda Maunes, wata mai gidan sayar da abinci a birnin Cebu.

“A baya muna sayan kilo biyu zuwa uku na albasa a rana. Amma a yanzu rabin kilo muke saya saboda shi ne daidai karfin mu,’’ in ji Ms Maunes a tattaunawar ta da BBC.

"Kwastomomin mu sun fahimci hakan saboda abin bai tsaya ga gidajen sayar da abinci kaɗai ba...magidanta ma na shan wahala saboda albasa ba ta isa a abincin da suke dafawa,’’ in ji ta.

Ɗandanon girkin gidan sayar da abinci na Filipino da ake gani na ƙara nuna tashin farashin kayayyaki.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da hauhwarar farashin kayayyaki kama daga abinci da man fetur wanda rabon da a ga haka ya ɗauki tsawon lokaci a ƙasar.

Shugaba Ferdinand Marcos Jr, wanda shi ne sakataren harkokin gona, ya kira batun tashin farashin kayayyaki da cewa ‘‘lamari ne na gaggawa’’. A farkon wannan wata, Mista Marcos ya amince da shigo da albasa masu launin ja da ruwan ɗoruwa a wani mataki na farfado da samar da shi.  

Masana sun ce sake buɗe harkokin tattalin arzikin ƙasar ta Philippines na janyo hankalin masu buƙata, yayin da tsananin yanayi ya shafi aikin samar da abinci haɗe da albasa.

"A watan Agusta, Sashin aikin gona ya yi hasashen cewa za a samu ƙarancin albasa. Watanni kaɗan bayan nan, ƙasar ta faɗa bala’in guguwa guda biyu da suka janyo lalacewar amfanin gona, a cewar Nicholas Mapa, wani babban masanin tattalin arziki a bankin ING.

"Mun kuma ga ƙarin masu buƙatar kayayyakin a lokacin da tattalin arziki ke farfaɗowa da sauri,’’ in ji mista Mapa.  

Tasirin hauhawar farashin kayayyaki

Tashin farashin kayayyaki ya shafi wuraren sayar da abinci da dama a birnin Cebu, wanda birni ne da ke cike da masu yawon buɗe ido.

Kayayyakin abinci irin naman ruwa da kayan lambu, yawanci ana amfani da su ne tare da albasa da kuma sauran kayan haɗi na girki.

"Albasa muhimmiyar abu ce a girki da muke amfani da ita. Tana ƙara ɗanɗano ga abinci,’’a cewar Alex Chua, wanda ke amfani da albasa a wurin da yake sayar da abinci.  

"Mun gode wa gwamnati saboda matakai da take ɗauka na rage hauhawar farashin kayayyaki. Muna fatan za su ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakai domin sauko da farashi,’’ in ji Alex.

An buƙaci ƙarin albasa, inda bayan nan ne April Lyka Biorrey, ta zaɓi rike ɗaurin albasa a ranar bikin aurenta da aka yi a birnin Iloilo.

"Na tambayi mijina ko za mu iya amfani da albasa maimakon furanni, tun da bayan aure su furanni jefar da su za a yi,’’ in ji ms Biorrey a tattaunawarta da wani gidan jarida.  

"Don haka me ya sa ba albasa ba? Tana da muhimmanci saboda ko bayan aure za  a iya amfani da ita,’’ in ji ta.

Wasu mutane da dama sun shiga damuwa bayan shigo da albasa cikin ƙasar.

A farkon wannan wata, an yi bincike kan wasu mambobin 10 na jirgin ƙasar ta Philippines kan yunkurin shigo da albasa da kuma kayan itace wanda ya kai kilo 40.

Daga baya, jami'an fasa kwabri sun ce mutanen ba zasu fuskanci tuhuma ba amma ta gargaɗi matafiya kan ɗaukar kayan amfanin gona ba tare amincewar hukumomi ba.

Matsin lamba

Hauhawar farashin ya sanya matsin lamba kan shugaba Marcos, wanda ya yi alkawarin bunƙasa bangaren samar da abinci a matsayinsa na sakataren aikin gona. Wasu ‘yan majalisa sun yi kira ga shugaban da ya naɗa wanda zai maye gurbinsa.

Da take magana kan batun tashin farashin kayayyaki a ƙasar, Sanata Grace Poe, ta ce “Kafin yanzu sikari ce ta yi tsada, yanzu kuma albasa. Watarana za mu tashin da jin cewa dukkan abubuwan amfani musamman girki sun yi tashin gwaron zabo.”

Marie-Anne Lezoraine, daga kamfanin bincike kan hada-hadar kasuwanni, ta ce suayin yanayi na cikin manyan abubuwan da ke barazana ga bangaren samar da abinci a ƙasar.

"Samun kuɗaden sayan kayayyaki na wahala ga mutane. Idan sauyin yanayi ya janyo ƙarancin abinci da tashin farashi, hakan zai yi tasiri mara kyau ga yawancin mutane a Philippines,’’ in ji miss Lezoraine.

Sai dai, mista Mapa na da yakinin cewa farashin albasa zai daidaita tun da gwamnati ta fara shirin shigo da shi ƙasar.  

"Sai dai, lokacin shigo da albasan ya zo kan gabar girbe amfanin gona a watan Febrairu ga manoma da ke cikin ƙasar,’’a cewarsa.  

"Farashin kayayyaki zai sauka da zarar an girbe amfanin gona da kuma kai kayan kasuwa don sayarwa.’’