Wani hari da aka kai a harabar majalisar dokokin Amurka da ke Washington DC ya yi sanadin mutuwar dan sanda guda tare da raunata wani wanda ake yi wa jinya a asibiti.
Wata mota ta afkawa shingen tsaron da aka kafa kafin daga bisani direban ya far wa jami'an da wuka, a cewar 'yan sanda.
'Yan sanda sun bude masa wuta kuma nan take maharin ya mutu.
Sai dai mahukunta sun ce harin wanda ya ke zuwa bayan watanni uku da barkewar tarzoma a majalisar dokokin Amurk , ba shi da alaka da ta'addanci.
"Ko da hari ne aka kai wa jami'an 'yan sanda ko wani, alhaki ya rataya a kanmu wajan gano dalilin daya sa aka yi haka kuma za mu bi diddigi", a cewar mukaddashin shugaban 'yansanda na Washington DC, Robert Corilee
Wasu majiyoyin tsaro da ke gudanar da bincike a kan al'amarin sun shaida wa kafar watsa labarai ta CBS cewa wani matashi mai shekara 25 mai suna Noah Greene ne ya kai harin.
Akasarin 'yan majalisar dokokin ba sa cikin ginin saboda sun tafi hutun bikin easter.