BBC Hausa of Friday, 9 April 2021

Source: BBC

De Bruyne ya tsawaita kwantiragin ci gaba da wasa a Etihad

Kevin De Bruyne zai ci gaba ci gaba da taka leda a Manchester City zuwa karshen kakar 2025 Kevin De Bruyne zai ci gaba ci gaba da taka leda a Manchester City zuwa karshen kakar 2025

Kevin De Bruyne ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Manchester City zuwa karshen kakar 2025.

Tun farko dan kwallon mai shekara 29 dan kasar Belgium yana da sauran kwantiragin fiye da shekara biyu a Etihad.

De Bruyne ya lashe kofin Premier League biyu da FA Cup da League Cup hudu tun bayan da ya koma City daga Wolfsburg a shekarar 2015.

Dan kwalllon tawagar Belgium yana daga cikin kashin bayan da Manchester City ke taka rawar gani a bana da ta kai take harin lashe kofi hudu a bana.

City ta kai wasan quarter finals a Champions League, inda ta doke Borussia Dortmund da ci 2-1 a wasan farko da suka buga ranar Talata.

Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama tana ta daya a kan teburin Premier da tazarar maki 14 tsakaninta da Manchester United ta biyu.

Haka kuma City ta kai wasan daf da karshe a FA Cup a bana da karawar karshe a Caraboa Cup da za ta fafata da Tottenham cikin watan Afirilu.

Duk da cewar De Bruyne ya yi fama da jinya a bana, hakan bai hana shi cin kwallo takwas ba, ya kuma bayar da 16 aka zura a raga a wasa 33 da ya yi a bana.