BBC Hausa of Sunday, 19 November 2023

Source: BBC

De Gea ba zai koma Saudiyya ba, kungiyoyi biyar na son Miller

David de Gea David de Gea

Tsohon golan Faransa, David de Gea, mai shekara 33, ya ki amincewa da tayin albashin fam 500,000 a kowanne mako idan ya amince komawa kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya inda zai hade da abokin taka ledarsa a kungiyar Manchester United. (Sun)

Inter Miami na daga cikin kungiyoyin da suke zawarcin De Gea, sun yi masa tayin komawa can kasancewar babu wani kulub da ya ke yi wa aiki tun bayan barin kungiyar Manchester United a kakar wasan da ta gabata. (Star)

West Ham ta bi takwararta, Newcastle a zawarcin dan wasa Kalvin Phillips, bayan kungiyarsa ta Manchester City ta amince saida dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 27, ko dai bashi ko aro ko ma din-din-din a watan Junairu. (Football Insider)

Fulham ka iya sake sabon lale kafin dauko dan wasan RB Leizpig, kuma mai kai hari na Jamus Timo Werner, dan shekara 27, idan an bude kasuwar saye da saida ‘yan wasa a watan Junairu. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Croatia Luka Modric, 38, ya yanke shawarrar komawa taka leda a Pro League din Saudiyya, idan kwantiraginsa da Real Madrid yak are a kakar wasa mai zuwa. (Sport - in Spanish)

Newcastle United na duba yiwuwar dauko mai kai hari na Guinea, da ke taka leda a Stuttgart Serhou Guirassy, mai shekara 27.(Football Insider)

Kungiyoyin Tottenham, Aston Villa, Newcastle, Brighton, Brentford da West Ham na daga cikin masu zawarcin dan wasan tsakiya na Scotland mai taka leda a Motherwell, Lennon Miller mai shekara 17. (Teamtalk)

Tottenham ma na sanya ido sosai akan dan wasan tsakiya na Sunderland Jobe Bellingham, mai shekara 18, wanda kani ne ga dan wasan Ingila Jude. (Football Insider)

Dan wasan gaba na Tottenham, Alejo Veliz na cikin wadanda ake kyautata zaton Kulub Bologna na Siri, ya yin da dan wasan na Argentina mai shekara 20, bai yi nasara kan shugaba Ange Postecoglou, a Shirin da ya dade ya na yi na barin kungiyar zuwa Rosario Central. (Calciomercato - in Italian)

Manchester United ta dauki wani kamfani mai mazauni a Los Angeles, da za su taimaka wajen horar da sabbin ‘yan wasan da suke Shirin saya nan ba da jimawa ba. (Sun)