BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Duniya na fuskantar haɗarin ƙarancin abinci sakamakon ƙarewar yarjejeniyar fito ta Ukraine

File foto File foto

A ranar Litinin din nan ne wa’adin yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta wajen kullawa, wadda ta kawo karshen hanawar da Rasha ta yi ta fitar da kayan abinci daga tashoshin jirgin ruwa na Ukraine ta tekun Bahar Aswad ta kare.

Tun kafin ranar Rasha take ta barazanar ficewa daga yarjejeniyar, wadda idan aka ki tsawaita ta, lamarin zai kara munana matsalar rashin wadataccen abinci a duniya.

Ana fargabar idan ba a sbunta ta ba al’amura za su munana dangane da samar da abinci ga al’ummar duniya saboda matsayin Ukraine na zama daya daga cikin manyan kasashen da ke samar da abinci a duniya.

Tun bayan da aka kulla yarjejeniyar, bayan da aka yi ta kai gwauro ana kai mari kafin a karshe Rasha ta amince da ita, ta bayar da kafar fitar da kayan abinci na tsaba sama da tan miliyan 32 na masara da alkama da sauran nau’in abinci daga Ukraine.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, samar da kayan abu ne da ya zama madogara wajen tallafa wa harkar samar da abinci ga duniya, wanda hakan ya kare ta daga fadawa mummunan yanayi na rashin abincin.

A karkashin wannan yarjejeniya wadda aka yi bayan da Rasha ta mamayi Ukraine, an samu damar jigilar kayan abincin na tsaba, sama da dakon jirgin ruwa 1000.

To amma daga Litinin din, kila ba za a sake ganin wani jirgin ruwan ba dauke da kayan abincin muddin ba a sabunta wannan yarjejeniya ba, domin jirgin ruwa na dakon abincin na karshe, wanda ke da rijistar kasar Turkiyya ya bar tashar Odesa ta kasar ta Ukraine, inda ya nufi birnin Santambul na Turkiyyar.

Rashar dai wadda ita ma kamar makwabciyar tata take ta zama daya daga cikin manyan masu samar da kayan abinci ta ce ba za ta sabunta wannan yarjejeniya ba har sai an biya mata bukatunta game da fitar da tata cimakar.

Da kuma sauran kayayyakin da take fitarwa ciki har da takin zamani.

Zuwa yanzu hukumomin Ukraine ba su ce komai ba dangane da wannan hali da ake ciki, da kuma korafin na Rasha, wanda Shugaba Putin ya nanata a ranar Asabar a tattaunawarsa ta waya da Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu.

Ya ce, ba a aiwatar da babban tsarin yarjejeniyar, wato samar da abincin, tsaba ga kasashe da ke cikin bukata, da suka hada da na Afirka.

Shugaban ya soki Ukraine kan rashin kai abincin ga kasashe masu tasowa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 47 ciki dari na tsabar abincin ta Ukraine an kai kasashe ne masu arziki da suka hada da Sifaniya ta Italiya.

Sai kashi 26 cikin dari da inda kasashe masu bi musu, wato na tsaka-tsaki a karfin arziki, kamar su Turkiyya da China.

Yayin da kashi 27 cikin dari na kayan abincin ya je ga kasashen da suke kutal, da tsaka-tsaki kutal a arziki kamar su Masar da Sudan.

To amma kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yarjejeniyar fitar da abincin ta amfani mutane a fadin duniya saboda a cewarta, ta samar da karin abinci ga kasuwar duniya, wanda a dalilin hakan farashi ya ragu.

Haka kuma Rashar na son a sanya bankinta, Rosselkhozbank – wanda ke gudanar da harkokin cinikinta na amfanin gona, cikin tsarin gamayyar bankunan da ake hada-hadar biyan kudade a duniya.

A farkon wannan shekara Tarayyar Turai ta ce ba ta tunanin sake mayar da bankunan Rasha da aka sanya wa takunkumi saboda mamayar da kasar ta yi wa Ukraine cikin tsarin bai daya na duniya.

Sai dai a ranar Juma’a Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce yana da kwarin gwiwa za a sake tsawaita yarjejeniyar bayan ya yi magana da Shugaba Putin.