BBC Hausa of Wednesday, 18 January 2023

Source: BBC

Elon Musk na fuskantar shari'a kan sakon da ya janyo wa masu hannun jarin Tesla asarar biliyoyin dala

Elon Musk Elon Musk

An fara wata shari'a kan wani sakon da attajiri Elon Musk ya wallafa a Tiwita, wanda a ciki ya yi ikirarin cewa zai saye dukkan hannayen jarin Tesla.

A ranar Talata aka fara shari'ar kan ikirarin na Mista Musk cewa zai biya masu rike da hannayen jarin kamfanin da kera motoci masu amfani da lantarki dala biliyan 72.

Masu hannayen jarin ne suka kai karar Mista Musk, suna cewa ya yi katsalandan cikin kasuwar hannayen jarin kamfanin, lamarin da suka ce ya sa sun tafka asara.

A shekarar 2018, ya wallafa wani sako a Tiwita cewa ya samo kudaden da zai biya dukkan masu rike da hannayen jarin kamfanin kudadensu domin kamfanin ya koma hannunsa shi kadai.

Sai dai hakan bai faru ba - kuma ba a saye hannayen jarin daga masu rike da su ba.

Masu rike da hannayen jarin sun ce wannan matakin na Mista Musk ya sa sun tafka asarar biliyoyin dala bayan da farashin hannun jarin na Tesla ya fadi kasa warwas.

Sai dai shugaban kamfanin ya kare kansa, yana cewa a lokacin da ya wallafa sakon, ya dauka wani kamfanin zuba jari na Saudiyya zai ba shi kudaden saboda haka bai aikata wani laifi ba.

Idan kotun da ke sauraron karar a birnin San Francisco ta sami Mista Musk da laifi, tana iya umartarsa ya biya tarar biliyoyon daloli baya ga wata dala miliyan 20 da tun da farko ya biya.

Kamfaninsa na Tesla ma sai da ya biya dala miliyan 20.