Everton na son sayo ɗan wasan Manchester United da Sweden da ke buga gaba Anthony Elanga, mai shekara 21.
An fahimci cewa Everton ta yi ƙokarin siyan ɗan wasan a watan Janairu amma za ta ƙara yin ƙoƙari a bazarar nan, inda suke sa ran cewa za su iya shawo kansa ya koma kungiyar ta Merseyside.
Everton na buƙatar dabara wurin daukar 'yan wasa a wannan bazarar saboda yawan kashe kuɗaɗen da suka yi a ƙarƙashin Farhad Moshiri na nufin har yanzu ana iyakance su da dokokin kiyaye kashe kuɗi na Financial Fair Play.
'Yan wasan sun riga sun bar Goodison a wannan bazarar kuma har ila yau yana yiwuwa a sake sanya waɗansu a kasuwa don Sean Dyche da Kevin Thelwell su sami ƙarin kuɗin kashewa.
Elanga ya kasance ɗan wasan Man United tun 2014, inda ya buga masu wasanni 55, wanda hakan ba nuni ne ga kwarewarsa ba.
Masana na cewa akwai bukatar ya bar United in dai har yana son wasansa ya cigaba, ko dai a matsayin aro ko kuma na dindindin.