BBC Hausa of Monday, 30 January 2023

Source: BBC

Everton ta nada Dyche sabon kocinta

Everton ta nada tsohon kocin Burnley Sean Dyche a matsayin sabon kocinta Everton ta nada tsohon kocin Burnley Sean Dyche a matsayin sabon kocinta

Everton ta nada tsohon kocin Burnley Sean Dyche a matsayin sabon kocinta.

Kungiyar da ke birnin Liverpool ta kori Frank Lampard makon da ya wuce, ganin cewa tana zaune na 19 a teburin Premier League, bayan da West Ham ta doke ta 2-0.

Dama Dyche bai sake daukar wata kungiya ba, tun bayan da Burnley suka sallame shi a watan Afrilun bara, bayan ya shafe shekaru 10 dasu.

Jan aikin da ke gaban Sean Dyche a yanzu shi ne tsallakar da Everton daga kare wannan kaka a ukun karshe, yayin da ya rage saura wasanni 18.

Rabon da Everton ta ci wasa tun watan Oktoba, kuma a yanzu dangantaka ta kara tsami tsakanin masu kungiyar da kuma magoya bayanta.