You are here: HomeAfricaBBC2023 05 19Article 1770233

BBC Hausa of Friday, 19 May 2023

Source: BBC

FA Cup: Tierney ne zai busa wasan Man United da Man City

Paul Tierney  ne zai busa wasan hamayya tsakanin Manchester United da Manchester City Paul Tierney ne zai busa wasan hamayya tsakanin Manchester United da Manchester City

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta babbatar da wadanda zai busa wasan karshe a FA Cup tsakanin kungiyoyin Manchester a watan Yuni.

Paul Tierney ne zai busa wasan hamayya tsakanin Manchester United da Manchester City da za su kara a Wembley ranar 3 ga watan Yuni.

Tierney shine zai ja ragamar mutum bakwai da za su yi alkalancin karawar farko da kungiyoyin za su yi a wasan karshe a FA Cup.

City ta kwao wannan matakin bayan da ta ci Sheffield United 3-0 a wasan daf da karshe ranar 22 ga watan Afirilu.

United kuwa doke Brigton 7-6 ta yi a nugun fenariti, bayan da suka tashi 0-0 ranar 23 ga watan Afirilu.

United tana da FA 12, ita kuwa City tana da shida, bayan da Arsenal ce kan gaba a yawan lashe kofin mai 14 jimilla.

Alkalin, wanda ya busa wa United karawa hudu a bana, yana da kwarewa a alkalancin wasan karshe a FA Cup, wanda ya yi mataimaki a 2010 a wasan Chelsea da Portsmouth.

Wadanda za su rike labule sun hada da Neil Davies da Scott Ledger da mai jiran ko-ta-kwana, yayin da Peter Bankes ne alkali na hudu.

David Coote ne zai kula da VAR, yayin da Simon Long zai taimaka masa.

Alkalan da za su busa wasan karshe a FA Cup na 2023

Alkali: Paul Tierney

Mataimaka: Neil Davies da Scott Ledger

Alkali na hudu: Peter Bankes

Mai jiran ko-ta-kwana: Adrian Holmes

Mai kula da VAR: David Coote

Mataimakin mai kula da VAR: Simon Long