BBC Hausa of Thursday, 6 May 2021

Source: BBC

Father Mbaka: Malamin cocin da ya nemi a tsige Buhari ya ce an dakatar da shi daga aiki

Rabaran Fada Ejike Mbaka Rabaran Fada Ejike Mbaka

Fitaccen malamin addinin Kiristan nan da ke birnin Enugu a kudu maso gabashin Najeriya Rabaran Fada Ejike Mbaka ya yi zargin cewa shugabannin Cocin Katolika sun dakatar da shi daga wa'azi da sauran lamuran addini tsawon wata guda.

Malamin ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga mabiyansa wadanda suka tsunduma zanga-zanga bayan da aka kwashe kwana biyu ba su ga malamin ba.

Rabaran Ejike Mbaka ya yi zargin cewa shugaban cocin Enugu, Bishop Callistus Onaga, ya dakatar da shi daga aiki tsawon kwana 30.

A cewarsa, an kuma hana shi yin magana da kowa baya ga umarnin cewa ya fice daga birnin Enugu.

Malamin ya ce an dauki matakin ne sakamakon wasu kalamai da ya yi kan siyasa da kuma sanya albarka da ya yi wa Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da ke neman ballewa daga Najeriya.

A ranar Laraba ne mabiya malamin addinin na Kirista suka mamaye tituna a jihar Enugu suna zanga-zanga bisa zargin cewa an kama jagoran nasu.

Mutanen sun yi zargin cewa jagoran nasu ya ɓace ne 'yan kwanaki bayan ya nemi Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka daga muƙaminsa saboda ƙaruwar matsalolin tsaro a ƙasar.

Masu zanga-zangar na kiraye-kiraye ga cocin Catholic Bishop of Enugu da ta bayyana musu inda ya shiga.

Makusantansa sun faɗa wa dandazon mabiyansa da suka taru ranar Laraba cewa ba su sake ganinsa ba tun bayan da ya faɗa musu cewa zai je wata ganawa da Bishop Onaga kwana biyu da suka wuce.

Sai dai daga bisani mabiya Mbaka ɗauki sowar murna bayan da jagoran nasu ya bayyana jim kaɗan bayan sun gudanar da zanga-zangar.

Kira a tsige Buhari

A makon jiya ne Rabaran Fada Ejike Mbaka, ya ce ya kamata shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki idan ba haka ba a tsige shi.

Rabaran Fada Mbaka, wanda a baya a goyi bayan shugaban kasar, ya kara da cewa ya yi kiran ne saboda Shugaba Buhari ya gaza shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya.

Malamin Cocin ya bayyana haka ne a gaban dimbin mabiyansa a Enugu da ke Kudu Maso Gabashin Najeriya.

"Idan da a kasashen da aka ci gaba ne da tuni Shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa. Ku ambato ni a koina cewa na yi kira ga shugaba Buhari ya sauka daga mulki tun da girma da arziki.

Muna kuka ne saboda ba mu da jagora...idan ba za ka iya mulki ba, ka sauka ko a sauya ka...ko dai Buhari ya sauka da kansa ko kuma a tsige shi.."

Fada Mbaka ya kara da cewa duk da yake a baya ya goyi bayan Shugaba Buhari, ya yi hakan ne saboda a baya ya taka rawa "amma yanzu me ya sa ana kashe mutane amma babban jami'in tsarom kasa yana zaune bai ce uffan ba?"

A cewarsa 'yan bindiga suna kai hare-hare a kan kowanne bangare na kasar amma Shugaba Buhari ya gaza daukar matakin da ya dace domin shawo kan matsalar.

"Muna kira ga majalisar wakilai ta tsige shugaba Buhari. Idan kuma ta ki tsige shi ta koma fada da Fada Mbaka, to abin da ba su taba tunanin zai faru ba zai fada kan 'yan majalisar wakilai da na dattawa," in ji Malamin Cocin.