BBC Hausa of Monday, 8 May 2023

Source: BBC

Fulham ta kara yin kasa da Leicester a teburin Premier

Fulham ta doke Leicester 5-3 a Craven Cottage ranar Litinin Fulham ta doke Leicester 5-3 a Craven Cottage ranar Litinin

Fatan da Leicester City ke yi na ci gaba da buga Premier League a badi ya ci karo da cikas, bayan da Fulham ta doke ta 5-3 a Craven Cottage ranar Litinin.

Fulham ce ta fara cin kwallo ta hannun Willian a bugun tazara daga baya Carlos Vinicius da Tom Cairney kowanne ya ci daya.

Ana komawa zagaye na biyu ne Cairney ya kara na hudu na biyu da ya ci a fafatawar.

Daga baya ne Leicester ta zare daya ta hannun Harvey Barnes, tun kan nan Jamie Vardy ya barar da fenariti a minti na 66.

Willian ne ya ci wa Fulham kwallo na biyar a wasan, yayin da James Maddison ya zura kwallo a raga a bugun fenariti, saura minti tara a tashi daga wasan.

Daf da za a tashi ne Leicester ta ci na uku ta hannun Barnes a karawar ta mako na 35 a Premier League.

Da wannan sakamakon saura maki daya tsakanin Leicester City da 'yan ukun karshen teburi, bayan da Everton da Brighton da Nottingham Forest da Southampton ke wasa ranar Litinin

Fulham ta kawo karshen wasa uku da ta kasa nasara, amma ta ci gaba da zama ta 10 a teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da abokiyar hamayya Brentford ta tara.

Leicester City na neman maki ido rufe nan gaba, wadda za ta fafata da Liverpool da Newcastle United.