BBC Hausa of Monday, 1 January 2024

Source: BBC

Fushin matasa na ƙaruwa kan Biden saboda yaƙin Isra'ila

Joe Biden, shugaban Amurka Joe Biden, shugaban Amurka

Zaɓen shugaban ƙasar Amurka na 2024 na iya zama mafi rarrabuwar kawuna ga masu zaɓe a tarihi. Sai dai yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a Gaza, goyon bayan da Shugaba Joe Biden ke bai wa Isra'ila na sanya shi cikin tsaka mai wuya wajen magoya bayansa - musamman ma matasa masu zaɓe.

Abdul Osmanu, ɗan shekara 22, ba ya da tabbacin cewa zai iya sake kaɗa wa shugaba Biden kuri'a. Dalilin haka kuwa shi ne, ya ce saboda goyon bayan da gwamnatin Biden ke bai wa Isra'ila yayin da take ci gaba da lugudan wuta a Gaza.

"A matsayina na mai son zaman lafiya, Musulmi, kuma bakar fata, akwai tashin hankali ganin abubuwan da ake yi wa Falasɗinawa," in ji Osmanu, wanda aka zaɓa shugaban yankinsa a 2021. "Abu mai wahala ne, gareni, in zaɓi shugaban da yake taimakawa waɗanda ke kashe mutane."

Matashin mai zaɓen ɗan jihar Connecticut ya faɗa wa BBC cewa yana duba yiwuwar zaɓar wani ɗan takara na daban ba Biden ko Trump, ko kuma ya fasa yin zaɓe gaba-ɗaya a 2024.

Matakin yana da matukar wahala, sai dai, kamar shi - da sauran matasa masu zaɓe da yawa - ba sa son ganin an sake zaɓar Donald Trump.

Ƙaruwar matasa masu zaɓe na jam'iyyar Democrat, kamar Mista Osmanu, ta fito ƙarara sun fara raba-gari da Shugaba Biden kan batun Isra'ila da kuma rikicin Gaza. Abin damuwa ne ga ƴan Democrat, cewa adawa da suke yi da tsare-tsaren shi za su iya yin barazana gare shi musamman ma irin wanda ya samu a lokacin zaɓen 2020.

A cikin watanni biyu da suka gabata, matasa masu kaɗa kuri'a suna gani a labarai da kuma a shafukan sada zumunta hotunan yaƙi da kuma ɓarna a cikin Gaza. Adadin Falasɗinawa da suka mutu sun kai 20,000, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza da ke karkashin ikon Hamas.

A lokaci guda, sun kalli yadda Mista Biden ya fito fili ya goyi bayan yunkurin da Isra'ila ta yi na kawar da ƙungiyar Hamas bayan da su da ƙungiyoyin kawance suka kashe mutane 1,200 a Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba. Tana ci gaba da yin garkuwa da mutane kimanin 100 a Gaza.

BBC ta yi nazari kan binciken zaɓen kuma ta yi magana da matasa shida masu jefa kuri'a na Democrat da shirya zaɓe daga ko'ina a faɗin Amurka.

Bayanai da hirarraki sun nuna suna ƙaruwar rashin jituwar siyasa a tsakanin matasa masu jefa kuri’a gabanin zaɓen 2024.

Sai dai ofishin yaƙin neman zaɓen Biden ta ki cewa uffan.

Sai dai masu zaɓe ƴan shekara 18-29 da suka yi rajista sun ce sun fi goyon bayan Falasɗinawa kan Isra'ila, kamar yadda wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta New York Times da Siena ta nuna.

A cewar binciken, masu jefa kuri'a ƴan shekara 18-29 suna sukar Isra'ila da hare-haren da take kai wa Hamas a faɗin Gaza, yayin da tsofaffi ke da ra'ayi mai kyau game da ƙasar.

Kodayake mafi yawan masu jefa kuri'a - kashi 57 - ba su yarda da yadda Mista Biden ke goyon bayan Isra'ila a rikicin ba, matasan suna adawa da hakan.

Kimanin kashi 72 na masu zaɓe ƴan shekara 18-29 sun ki amincewa da ƙoƙarin Mista Biden, a cewar kuri'ar jin ra'ayin jama'a da jaridar Times da Siena suka shirya.

Anna Bosking, ƴar shekara 22, ta shirya sake zaɓar Mista Biden. Sai dai bayan yin karatu da ya shafi Siyasar Gabas Ta Tsakiya a jami'a, da take magana da abokan karatunta daga Gaza da kuma ganin shaidun mutane a kafofin sada zumunta, ta koma sukar dangantakar Amurka da Isra'ila.

"Kafin wannan rikicin na ɗauka cewa Isra'ila kawace da za mu marawa baya, kuma ban taɓa samun wata matsala ba," ta faɗa wa BBC. "Amma ina tunanin an tilastawa Amurkawa ɗaukar dangantaka ta tarihi a lamarin."

Abin da ya kawo rarrabuwar ra'ayoyi shi ne matasa ƴan Democrat, musamman ma ƴan progressives, za su iya haɗa gwagwarmayar ƙasar Falasɗinawa a yaƙi don samun ƴanci da ke faruwa a Amurka.

"Ƙungiyoyi da dama da nake cikinsu a yanzu sun bayyana irin mawuyacin hali da Falasɗinawa ke ciki, kuma ina son ci gaba da ɗaga gwagwarmayarsu," in ji Michael Abramson, ɗan shekara 25, kuma darektan ƙungiyar matasan Democrat a lardin Maricopa a jihar Arizona.

Mista Abramson yana shirya muhimman taruka na jam'iyyar Democrat a Arizona. Ya ce yana da kwarin gwiwa matasa za su fito a jihar Arizona domin zaɓar wasu ƴan takara - amma ya ce ba shi da tabbacin cewa ko shi da saura za su zaɓi ɗan takarar Democrat.

Jam'iyyar Democrat ta dogara ga matasa mazu zaɓe waɗanda suka fito suka kaɗa mata kuri'a kafin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2020 da kuma zaɓen tsakiyar zango a 2022.

Kuma ba dukkan matasa mazu zaɓe ne ke sukar goyon bayan da Mista Biden ke bai wa Isra'ila ba.

Jessica Schwab, ƴar shekara 20 - ɗaliba a jami'ar Columbia da ke birnin New York, ta ce ba ta son ganin an sake zaɓar Mista Trump kuma ta hakikance cewa Mista Biden na tafiyar da rikicin Gaza yadda ya kamata.

"Yana goyon bayan Isra'ila kuma yana ba su taimakon soji, da samar musu da kuɗaɗe a ɓangaren tsaro," in ji ta. "Amma ina son yadda yake kiran a dakar da buɗe wuta don kai agaji, da kuma ganin an rage yawan waɗanda suke jikkata a Gaza."

Masu goyon bayan Mista Biden sun kalubalanci cewa saura kusan shekara guda kafin zaɓen 2024, kuma matasa ƴan Democrat za su dawo ra'ayin jam'iyyar idan aka gabatar musu da zaɓi tsakanin Mista Biden da Mista Trump.

"Zaɓi ne tsakanin ƴan takara guda biyu," in ji Jack Lobel wani matashi ɗan ƙungiyar wayar da kan mazu zaɓe. "Yayin da tsare-tsaren Shugaba Biden a kan Gaza ke harzuka wasu matasa, hakan ba zai canja cewa shi da Donald Trump mutane ne daban-daban."