BBC Hausa of Sunday, 16 April 2023

Source: BBC

Ganduje ya yafe wa Kanawa

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga al'ummar jihar da su yafe masa.

Yayin da ya halarci Tafsiri a masallacin Al-Furqan da ke birnin Kano, gwamna Ganduje ya ce dole ya nemi afuwar Kanawa, kasancewar 'yan kwanaki ne kawai suka rage masa ya sauka daga mulki.

Ya ce shi a ɓangarensa ya yafe wa duk wanda ya ɓata masa rai, sannan shi ma yana neman duk wanda ya ɓata wa rai da su yafe masa.

''Wa'adina na mulkin jihar Kano ya zo ƙarshe, ina yi muku bankwana, kuma ina yi muku fatan alkairi, kuma waɗanda muka ɓata wa, dama babban malami ya faɗi muhimmancin yafiya'', in ji Ganduje.

Ya ƙara da cewa ''To ni na yafe, duk abin da wani ya faɗa game da ni, na yafe masa kowanne iri ne, ni ma kuma ina roƙo a yafe min''.

A wani tafsirin da ya halarta da Sheikh Nasidi Abubakar Gorondutse ya jagoranta, gwamna Ganduje ya ce ya kwashe shekara shida yana riƙe da muƙamin kwamishina a Kano.

''Sannan na rike muƙamin mataimakin gwamna na shekara takwas, sannan na kwashe shekara takwas ina riƙe da muƙamin gwamna, don haka dole na gode wa Allah kan wannan baiwa da ya yi min'', in ji gwamnan.

''A tsawon waɗannan shekaru dole na sani zan yi daidai a wasu wuraren, a wasu kuma na yi kuskure. A wani lokaci wani zai aikata kuskure a madadinka. Don haka duk wanda na yi wa ba daidai ba, ina neman afuwarsa da ya yafe mini''.

Tun bayan ɓullar bidiyoyin biyu ne al'ummar jihar ke ci gaba da tofa albarakacin bakinsu.