BBC Hausa of Saturday, 15 May 2021

Source: BBC

Gane Mini Hanya: 'Dalilan zuwan Hausawa kasar Oyo' - Sarkin Hausawan Sabo

Sarakunan Hausawa a kasan Yarabawa a shekarun baya Sarakunan Hausawa a kasan Yarabawa a shekarun baya



Latsa hoton da ke sama don sauraren hirar:

Hausawa na daya daga cikin al'ummar Afirka ta yamma da ke da yawan yawo a sassan duniya musamman sakamakon fatauci.

Wani yanki da Hausawa suka yi wa tsinke shi ne kudancin Najeriya musamman kudu maso yammaci wato yankin Yarabawa.

Birnin Badin na jihar Oyo na daya daga cikin wurare na farko-farko da Hausawan suka yi wa tsinke.

A hirarsa da wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai, Alhaji Hassan Isiyaka wanda shi ne Sarkin Hausawan Sabo da ke birnin na Badin ya ce Hausawa sun je birnin ne shekaru kusan 200.