BBC Hausa of Wednesday, 26 July 2023

Source: BBC

Gasar cin kofin duniya: Sifaniya da Japan sun kai zagaye na biyu

Yan wasan Sifaniya Yan wasan Sifaniya

Sifaniya ta caskara Zambia 5-0 a wasa na biyu a cikin rukuni a gasar cin kofin duniya ranar Laraba.

Sifaniya ta fara da nasara a rukuni na uku, bayan da ta doke Costa Rica 3-0 a makon da ya gabata, wadda ta kai hare-hare 46 a ragar Costa Rica.

Japan ma ta kai zagaye na biyu a rukuni na ukun, bayan da ta yi nasara a kan Costa Rica da ci 2-0.

Ranar Litinin za a buga wasan karshe a rukuni na uku, inda za a kece raini tsakanin Japan da Sifaniya.

Daya wasan za a yi ne tsakanin Zambia da Costa Riga.

Zambia, wadda ke wakiltar Afirka a karon farko a gasar kofin duniya ta mata, an zura mata kwallo 10-0 a wasa biyun da ta buga a cikin rukuni.

Ranar Asabar a wasan farko a rukuni na uku, Japan ta doke Zambia da cin 5-0.

Wadanda ke wakiltar Afirka a wasannin da ake yi a Australia da New Zealnad, sun hada da Zambia da Morocco da Afirka ta Kudu da kuma Najeriya.