Kusan mutane 200 sun mutu a Turkiyya da Syria sakamakon girgizar kasa mai karfi da ta afkawa gidajen jama'a.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afkawa yankin Gaziantep da ke kudancin Turkiyya a tsakiyar dare.
Kuma an jiyo ruguginta har daga Gaza. An kuma samu rushewar gidaje a Lebanon.
Turkiyya dai ta ayyana dokar ta baci tare da kira ga mutane su dakatar da amfani da wayoyinsu, saboda masu aikin agaji su samu damar kai wa ga wadanda suka makale a cikin baraguzai.
A 1999, irin wannan mummunar girgizar kasar tayi ajalin mutane dubu 17.